Likitoci sun yi barazanar komawa yajin aiki

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa sun yi barazanar komawa yajin aiki a duka asibitocin gwamnati da ke kasar nan, idan ba a biya mambobinsu hakkokinsu ba, kamar yadda Shugaban Kungiyar  Dokta Adamu Askira ya bayyana. Hakan yana zuwa ne kwana uku bayan likitocin sun janye wani yajin aiki da suka shiga. Shugaban ya ce ya […]

Likitoci sun yi barazanar komawa yajin aiki

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa sun yi barazanar komawa yajin aiki a duka asibitocin gwamnati da ke kasar nan, idan ba a biya mambobinsu hakkokinsu ba, kamar yadda Shugaban Kungiyar  Dokta Adamu Askira ya bayyana.

Hakan yana zuwa ne kwana uku bayan likitocin sun janye wani yajin aiki da suka shiga. Shugaban ya ce ya umarce ‘ya’yan kungiyarsu da su koma yajin aiki idan har ba a biya su hakkokinsu zuwa a ranar Asabar da ta gabata.

Likitocin dai sun yanye yajin aiki ne a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan wani taron kwamitin zartarwar kungiyar a garin Keffi na Jihar Nasarawa.