Likitoci sun yi wa tsoho tiyata ya koma kamar saurayi

Adadin mutanen da ke fita ketare domin tiyata kusan ya ninka a fiye da shekara hudu da suka gabata.

Likitoci sun yi wa tsoho tiyata ya koma kamar saurayi

Fuskar Michael kafin da kuma bayan an yi masa tiyatar

Masu amfani da kafar sadarwar zamani ta X (Twitter), sun yi ta sharhi cikin mamaki, bayan da likitoci suka yi wa wani mai suna Michael tiyatar fata inda ya bi matakan tiyatar guda takwaskuma sakamakon karshe ya canza halittarsa zuwa fuskar saurayi mai shekara 30.

Likitocin tiyatar fata na Turkiyya sun kammala gagarumin sauyi a fuskar Michael – ta yadda wasu ke ganin cewa yanzu ya koma kamar mai shekara 30.

Este Med Instabul da yake bayyani a shafin Instagram ya ce: “Mun yi wa Michael gyaran fuska, wuya da tiyatar fatar ido ta kasa da sama, rage kitsen fuskar da tiyatar gyara karan hanci da hanyoyin dashen gashi.

“Ya samu canji mai ban-mamaki, kuna iya gani daga hotunansa.”

Hoton Michael gabanin a yi masa tiyatar

Hotunan tiyatar masu dauke da Michael kafin tiyatar da kuma bayan tiyatar sun yi tashe jim kadan bayan an wallafa a shafin sada zumunta na X inda miliyoyin masu amfani da kafar suka rika sharhi a kai.

Aminiya ta ruwaito cewa, an wallafa sakon mai taken: “Likitocin fata na Turkiyya sun shahara bayan tiyata sau 8 a lokaci daya… mutumin nan ya dawo saurayi dan shekara 30.”

Cikin mamakin tsarin tiyatar Michael, wani mai amfani da kafar X ya yi martani da cewa: “Lokacin da nake shekara 55, tabbas zan je can in sake zama dan shekara 30.”

Wani kuma ya ce, “To… Na san inda zan je nan da shekara 10 daga yanzu lokacin da nake bukatar sauyin fuska. Turkiyya da Koriya ta Kudu suna kafada-dakafada idan ana batun gyaran fuska.”

Yayin da na uku ya ce: “Ka yi tunanin wannan fasaha a cikin shekara 20 zuwa 30 lokacin da dukanmu muka fara bukatar kwalisa…” Ofishin Kididdiga na Kasar (ONS) ya kiyasta cewa adadin mutanen da ke tafiya kasashen waje don yin tiyata kusan ya ninka a fiye da shekara hudu, inda mazauna Birtaniya 248,000 suka zabi zuwa a cikin 2019 idan aka kwatanta da 120,000 a shekarar 2015.

A shekarar 2022 kadai Turkiyya ta karbi ’yan yawon bude-ido na Birtaniya miliyan 1.2.

Yawanci asibitocin tiyatar fata 913 suna karbar baki, gami da wadanda aka canja wa filin jirgin sama, otal otal har ma da masu zirgazirga, wanda ba za a iya kashe kasa da Fam 3,000 (kimanin Naira miliyan 5 da 698 da 734) don yin aikin tiyatar.

Fuskar Michael kafin da kuma bayan an yi masa tiyatar

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja