Likitoci sun yi wa yara 65 kaciya kyauta a Zariya
Kungiyar ta kuma ce za ta yi wa mutum 200 tiyata kyauta.
Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) reshen Jihar Kaduna, ta tallafa wa al’ummomin unguwar Cikaji da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Zariyan Jihar Kaduna.
Likitocin sun kuma yi wa yara akalla 64 kaciya kyauta a yankin domin bikin makon lafiyar da suke yi na bana.
- Zanga-zangar kin jinin rigakafin COVID-19 ta kara zafi a Belgium
- An tsinci gawar yara 8 a cikin tsohuwar mota a Legas
Shugaban kungiyar likitocin, Dokta Umar Musa ya ce za su tallafa wa mutane sama da 200 wajan duba lafiyarsu, tare da yi musu tiyata kyauta.
A cewarsa, cututtukan da za a yi musu tiyatar sun hada da kaba da kari da sauran kananan cututtuka, da kuma yi wa yara kaciya, tare da raba musu magunguna kyauta.
Dakta Umar ya ce sun yi kasafin kudi har Naira miliyan biyu don gudanar da aikin, kuma ya ce a kashin kansu suke tara kudaden ta hanyar yi wa juna haraji daga albashinsu.
Daya daga cikin iyayan yaran da suka amfana da kaciyar ta nuna jin dadinta ta yadda aka taimaka musu kuma aka basu magunguna a lokacin da ya kamata.