Likitoci sun yin dashen mahaifar gawa an haihu da ita
Likitoci a Sao Paulo, ta kasar Brazil sun yin nasarar dashen mahaifar wata gawa ga wata mace inda matar ta haifi wata lafiyayyiyar jaririya. Likiocin sun yi nasarar dashen mahaifar ce bayan shafe sa’o’i 10 suna yin tiyata. Mahaifiyar jaririyar mai shekara 32 an haife ta ce ba tare da mahaifa ba bayan da kuma […]
Likitoci a Sao Paulo, ta kasar Brazil sun yin nasarar dashen mahaifar wata gawa ga wata mace inda matar ta haifi wata lafiyayyiyar jaririya.
Likiocin sun yi nasarar dashen mahaifar ce bayan shafe sa’o’i 10 suna yin tiyata. Mahaifiyar jaririyar mai shekara 32 an haife ta ce ba tare da mahaifa ba bayan da kuma tana da juna biyu.
Likitocin sun yi dashen mahaifa sau 39 kuma dukan mahaifar na rayayyun ne, an kuma yi wa wadansu iyaye mata dashe an samu nasarar haihuwar jarirai 11.
Yayin da ita kuwa wannan matar da ba ta da mahaifa an yi mata dashen mahaifar har sau 10 amma ba a samu nasara ba, sai dai kawai idan an yi ta yi ta bari, an gwada mahaifar gawa amma ba a samu nasara ba. Daga bisani, an yi amfani da mahaifar wata mata mai ’ya’ya uku wadda ta rasu bayan ta yi fama zubar jini sakamakon cutar kwakwalwa da ta same ta. Hakan ya sa likitocin suka yi nasarar dashen mahaifar matar da ta rasu, wanda hakan ya sa aka haifi jaririyar.
A binciken likitocin kamar yadda wanda ya jagoranci tiyatar Dokta Dani Ejzenberg, na asibitin Faculdade de Medicina da ke garin Sao Paulo ya nuna cewa a duk cikin mata 4,500 daya na iya samun irin wannan matsala ta rashin mahaifa da ake kira Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser.