Likitoci za su shiga yajin aiki kan rashin isassun ma’aikata a Kano

Ƙididdigar ƙungiyar ta nuna yadda kowane likita yake duba marasa lafiya 33,000 a jihar.

Likitoci za su shiga yajin aiki kan rashin isassun ma’aikata a Kano

Likitoci a Jihar Kano, sun bayyana damuwarsu kan rashin isassun likitocin da za su ke duba marasa lafiya, wanda hakan ya sa suke shirin tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Ƙungiyar Likitocin Asibitocin Gwamnati da Likitocin Haƙora ta Ƙasa ce, ta bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da sakataren ƙungiyar, Dokta Anas Idris Hassan, ya jagoranta.

Ya ce gwamnatin jihar ta amince a watan Yuni za ta biya musu buƙatunsu, amma har yanzu ba ta ɗauki wani mataki ba.

Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suke korafi a kai shi ne rashin biyansu alawus bayan wucewar annobar COVID-19, wanda Gwamnatin Tarayya ta biya tun a 2021, amma Gwamnatin Jihar Kano har yanzu ba ta biya ba.

Dokta Anas ya kuma bayyana cewa likitocin da aka ɗauka aiki a watan Satumban 2023 ba su samu albashinsu ba.

Likitocin sun kuma koka kan yanayin asibitocin Kano da rashin manyan kayan aiki.

Babbar matsalar ita ce ƙarancin likitocin da za su ke duba marasa lafiya.

A Kano, akwai kimanin mutum miliyan 20, amma likitoci 600 ne kawai suke duba su, wanda hakan ke nufin likita ɗaya na kula da marasa lafiya 33,000.

Wannan adadi ya saɓa da ƙa’idar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara.

Saboda waɗannan matsaloli, likitocin suka yanke shawarar tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou