Likitoci za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Sun ce dole gwamnati ta cika alkawarin da ta yi musu a baya

Likitoci za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Likitoci

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta kasa ta yi barazanar sake shiga yajin aiki daga ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.

Kungiyar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Dakta Aliyu Sokomba, Sakatarenta Dakta Bilqis Mohammad, da Sakataren Yada Labarai, Dakta Egbogu Stanley, ta ce za ta shiga yajin aikin ne bayan da wa’adin kwana 21 da ta ba gwamnati sun kare ranar 17 ga watan Agusta.

Likitocin dai na bukatar Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da su, ta kuma biya su kudaden alawus-alawus na yaki da annobar COVID-19 da kuma basukan albashin da suke bin ta na shekarun 2014, 2015 da 2016.

Idan za a aiya tunawa, a ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata ne kungiyar ta fara wani yajin aikin sai baba ta gani kafin daga bisani ta janye shi ranar 22 ga watan bayan da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki susa ka baki.

Kungiyar ta ce, “Majalisar Zartarwar kungiyarmu ta yanke shawarar shiga yajin aiki daga karfe takwas na safiya ranar Litinin, 7 ga watan Satumbar 2020, har sai an cika wadannan sharudda; biyan mu kudaden horon neman kwarewa da muke bi kamar yadda aka amince a kasafin kudin 2020 da aka yi wa kwaskwarima; da samar da ingantaccen tsarin inshorar lafiya ga dukkannin ma’aikatan lafiya.

“Kazalika, sai an biya mu bashin kudaden alawus din aikin annobar COVID-19 da muke bi; sabunta biyan kudaden alawus da aka amince za a biya mu a tattaunawarmu ta baya da masu ruwa da tsaki; biyan mu gibin albashin da muke bi na shekarun 2014, 2015 da 2016,” inji kungiyar.

Likitocin sun kuma ce dole a biya dukkannin masu aiki a cibiyoyin lafiyar manyan makarantun gwamnatin tarayya da na jihohi hakkokinsu kamar yadda sabon tsarin biyan mafi karancin albashi ya yi tanadi.

Galibi dai kungiyoyin ma’aikata kan shiga yajin aiki domin neman wasu hakkokinsu a Najeriya, wada hakan ke zama hanya daya tilo da hukumomin ke share musu hawaye.