Likitocin Najeriya Sun Koka Kan Yadda Ake Bautar Da Su A Birtaniya

Wasu likitocin Najeriya da suka koma aiki da asibitocin Turai sun koka kan yadda ake bautar da su a Birtaniya.

Likitocin Najeriya Sun Koka Kan Yadda Ake Bautar Da Su A Birtaniya

Likitan Najeriya

Wasu likitocin Najeriya da suka koma aiki da asibitocin Turai sun koka kan yadda ake bautar da su a Birtaniya.

A wani rahoto na musamman da Sashen Binciken Kwakwaf na BBC ya fitar, ya bankado yadda likitocin Najeriya da aka dauka aiki a asbitoci masu zaman kansu a Birtaniya suke rayuwa cikin bauta fiye da wacce suka bari a Najeriya.

Guda daga likitocin da suka samu aiki a wani asibiti mai zaman kansa mai suna Nuffield Health Leeds, Augustine Enekweci, ya ce yana ji tamkar a kurkuku yake rayuwa saboda wahalar da yake sha a asibitin.

“Ina aiki ne tsawon awanni 24 a sati, kuma ba ni da ikon barin harabar asibitin ko nan da can.

“Mafi yawan lokuta gajiya na yi min yawa har na dinga tsoron halin da zan shiga da marasa lafiyan da nake dubawa,” in ji Enekwechi .

A hannu guda kuma hukumar gidanarwar asibitin Nuffield din ta musanta wannan batu, inda ta ce suna bai wa dukkanin likitocin hutu, har tsakanin canjin aiki, hadi da musayar aiki idan bukatar hakan ta taso.

Hukumar asibitin ta ce lafiyar ma’aikatansu na daga cikin abubuwan da suka fi bai wa muhimmaci a kodayaushe.

Murna ta koma ciki

Enekwechi dai ya samu aiki a asibitin Nuffield Health Leeds ne karkashin wani kamfani mai zaman kansa mai suna NES Healthcare, wanda ya yi suna wajen daukar likitoci zuwa kasashe ketare, musamman daga Najeriya.

Ya ce da farko ya yi matukar farin ciki da samun aikin, har ta kai bai tsaya duba dokokin kwangilar daukar ba.

BBC ta ce baya ga Enekweci, ta gano kusan kashi 92 cikin 100 na likitocin da aka dauka aiki a kasashen ketaren na fama da wannan matsalar, kuma kaso 81 cikin 100 daga cikinsu ’yan Najeriya ne.

Zaftare albashi

Baya ga aikin bauta, yawancinsu na kuka da zaftare musu kaso mai tsoka na albashinsu.

Daga ciki akwai wani likita mai suna Femi Johnson da shi ma ya bayyana yadda yake aiki tsawon sa’o’i 16 a rana, da kuma yiwuwar kiran sa aiki kowane lokaci.

“Na gaji matuka, kullum barci nake ji, aikin ma gagara ta yake wani lokacin.

“Amma da na bukaci hutu sai NES suka ce za a dinga cire kudin ranakun da na huta, domin asibitin su samo wanda zai yi aiki a madadina a ranakun.”

Wasu likitocin na NES sun ce sun sami taimako daga wata Dokta Jenny Vaughan ta Kungiyar Likitocin Birtaniya, bayan karbar korafe-korafe da yawa, inda ta ce tsarin kula da lafiyar Burtaniya ya rabu kaso biyu ne.

“Daya na likitocin da aka dauka karkashin tsarin NHS, dayan kuma na masu daukar ma’aikata na duniya da ke aiki a asibitoci masu zaman kansu.

“Sannan likitocin da aka dauka karkashin tsarin NHS ne kadai za a iya tsarawa aiki na tsawon awanni 48, idan kuma suka bukata a radin kansu har zuwa awanni 72 a mako.”

Ita ma dai Kungiyar Likitocin Birtaniya ta ce ta kadu matuka da jin wadannan korafe-korafe, sai dai za su tabbatar da asibitocin sun dawo aiki daidai da tsarin aiki na gwamnatin kasar.