Likitocin Saudiyya za su yi aikin tiyata kyauta a Sakwkato

Likitocin za su isa Sakkwato ranar Juma’a 8 ga watan Oktoban da muke ciki.

Likitocin Saudiyya za su yi aikin tiyata kyauta a Sakwkato

Likitocin Saudiyya da wasu kasashe za su gudanar da ayyukan tiyatar zuciya kyauta a Jihar Sakkwato.

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko, ya ce kwararrun likitocin, daga Kungiyar Musulmi ta Duniya da ke Saudiyya, za su iso Nejeriya ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Oktoban da muke ciki.

“A ranar da suka sauka a Najeriya za su wuce zuwa Sakkwato domin fara ayyuakn tiyata a zuciya kyauta,” inji Wamakko.

Sanarwar da ya fitar ta hannun hadiminsa kan kafafen sada zumunta, Bashar Abubakar,  ya ce likitoci da suaran jami’an lafiya 24 ne za su gudanar da ayyukan.

Ya ce tsohon gwamnan ne ya gayyato likitocin zuwa Jihar Sakkwato a matsayin gudummawa a mazabarsa ta Sakkwato ta Arewa.

Ya ce likitocin da sauran ma’aikatan lafiyan sun fito ne daga kasashe daban-daban da suka hada da kasar Saudiyya, Masar, Siriya, Filipin, Netherlands da sauransu.