Likkafar furodusa Mo Abudu ta kara dagawa

A farkon makon nan ne likkafar shahararriyar mai hada shirye-shiryen talabijin, Mo Abudu ta kara daukaka, bayan da mujallar ‘The Holywood Reporter’ ta ba da sanarwar zaben ta daya daga cikin hamshakan mata na duniya da suka kware wajen aikin jarida, musamman na shirin talabijin. Mujallar ta fitar da sanarwar ce a fitowar ta ta […]

Likkafar furodusa Mo Abudu ta kara dagawa

A farkon makon nan ne likkafar shahararriyar mai hada shirye-shiryen talabijin, Mo Abudu ta kara daukaka, bayan da mujallar ‘The Holywood Reporter’ ta ba da sanarwar zaben ta daya daga cikin hamshakan mata na duniya da suka kware wajen aikin jarida, musamman na shirin talabijin. Mujallar ta fitar da sanarwar ce a fitowar ta ta watan Oktoba.
Kamar yadda wannan mujalla ta kasance, duk matar da ta samu shiga cikin kundinta, to babu shakka ta kasance hamshakiya kuma shahararriya a fagenta ko sana’arta.
Ita dai Mo Abudu, wacce cikakken sunanta Mosunmola Abudu, ta shahara ne a fannin aikin jarida, kwararriyar mai hada shirye-shiryen talabijin ce kuma ga ta hamshakiyar ’yar kasuwa.
An haife ta ne a ranar 11 ga Satumba, 1964, wato a bana shekararta 49 ke nan a duniya. Kimanin shekaru goma ke nan da ta tsoma hannunta a harkokin kasuwanci a Najeriya, amma cikin wadannan shekaru ta shahara, ta kafa gidan talabijin mai zaman kansa, wanda ke tallata al’amuran kasuwanci, kamar kuma yadda take daga martabar mata.