Likkafar mawaki Tuface na kara dagawa
A guguwar nan mai kadawa, mawakin zamanin nan da aka fi sani da suna Tuface Idibiya yana ta kara samun daukaka a sana’arsa, duk kuwa da cewa yana gamuwa da abubuwan gutsuri-tsoma. A kwanan nan ne aka jiwo labarin ya samu kwantaragin talla a kamfanin layin wayar Airtel, inda suka biya shi kudi masu yawa, […]
A guguwar nan mai kadawa, mawakin zamanin nan da aka fi sani da suna Tuface Idibiya yana ta kara samun daukaka a sana’arsa, duk kuwa da cewa yana gamuwa da abubuwan gutsuri-tsoma. A kwanan nan ne aka jiwo labarin ya samu kwantaragin talla a kamfanin layin wayar Airtel, inda suka biya shi kudi masu yawa, wadanda bai bayyana wa ’yan jarida ba.
Mawakin wanda ya fara suna tun lokacin da ya fito da faifan wakarsa mai taken African kueen ya ci gaba da shahara har zuwa wannan lokaci, inda masoyansa, musamman ma mata suka rika nuna masa kauna a kowane lokaci.
Wani abu da ke kara yayata sunansa a duniyar mawaka shi ne, yadda ya kasance ya haifi ’ya’ya har biyar da mata daban-daban kuma ba tare da aure ba. Akwai mace ta farko, mai suna Sunmbo Ajaba, wacce ta haifa masa ’ya’ya maza guda biyu. Mace ta biyu mai suna Pero Adeniyi, ta haifa masa ’ya’ya biyu, daya mace, daya namiji. Sai kuma Annie Macaulay, wacce ta haifa masa yarinya daya, cikon ta biyar din.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a kwananan, Tuface ya yi bayani game da rayuwarsa ta soyayya, inda ya fadi cewa: “Ban gaji wannan tsarin rayuwar daga mahaifina ba, domin kuwa shi ba manemin mata ba ne. Na hakkake da wannan, domin kuwa ban taba kama shi da wata matar da ba ta aurensa ba. Ya kasance mai adalci ga mahaifiyata. Hakika na san cewa ina soyayya da mata da yawa a rayuwata, wannan kuma wani yanayi ne da ya kasance tare da ni, a matsayina na mawaki. A rayuwata, ban taba zaton zan yi soyayya da macen da ta wuce daya ba kamar yadda na kasance a yanzu. Duk da haka kuma ba na nadamar haka, ina kaunar ’ya’yana. A yanzu haka ina tare da mata uku, wadanda su suka haifa mini ’ya’yana guda biyar, wanda a yanzu haka ma daya na nan za ta haifa mini na shida.”