Limaman addinai sun zargi gwamnati da gazawa kan tsaro

kungiyar Malamai da Limaman Musulunci ta Najeriya ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da manyan jami’an tsaro su hanzarta magance matsalar tabarbarewar tsaro ko kuma su ajiye ayyukansu.A wata ganawa da manema labarai a Kaduna da kungiyar ta gudanar tare da hadin gwiwar kungiyar dalibai Musulmi shiyyar Arewa, malamai da limaman sun nuna damuwa […]

Limaman addinai sun zargi gwamnati da gazawa kan tsaro
Limaman addinai sun zargi gwamnati da gazawa kan tsaro

kungiyar Malamai da Limaman Musulunci ta Najeriya ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da manyan jami’an tsaro su hanzarta magance matsalar tabarbarewar tsaro ko kuma su ajiye ayyukansu.
A wata ganawa da manema labarai a Kaduna da kungiyar ta gudanar tare da hadin gwiwar kungiyar dalibai Musulmi shiyyar Arewa, malamai da limaman sun nuna damuwa bisa yadda gwamnati ke tunkarar batun hare-haren ta’addanci a kasar nan.
Malaman sun bukaci gwamnati ta yi wa jama’ar kasar cikakken bayani dangane da wasu a’’amurra da ke wakana masu nasaba da tsaron musamman batun wani jirgin sama daga Najeriya da aka kama dauke da dimbin kudi a Afirka ta Kudu.
A wani labarin kuma kungiyar Bishop-Bishop din Cocin Katolika ta kasa (Catholic Bishop Conference of Nigeria) ta ce Gwamnatin Tarayya ba ta yin abin da ya kamata wajen dakile ayyukan wuce gona da iri na kungiyar     Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Bishop-Bishop din sun kuma kalubalanci gwamnatin ta hanzarta bullo da dabarun kare rayuka da dukiyar al’umma a yankin.
A wata takardar bayan taro da suka gudanar a Warri ta Jihar Delta a ranar Alhamis din makon jiya Bishop-Bishop din sun nuna damuwa kan kazantar zubar da jini a yanki, inda suka bukaci gwamnati ta zage dantse don magance hakan.
Takardar dauke da sanya hannun Shugaban kungiyar Dokta Ignatius Kaigama da Sakatarenta William Abenya da aka tura jaridar Premium Times ta ce halin da ake ciki a yankin     Arewa maso Gabas yana kara habaka barazanar mamaye kasar nan.
Takardar ta ce: “Yayin da a wasu lokuta ake kai hare-haren da ake hallaka Musulmi da lalata dukiyarsu, Kiristoci da coci-cocinsu da sauran wadanda ba Musulmi bas u ne manyan wadanda ’yan Boko Haram suka fi kai wa hari don hallaka su.”
Ta kara da cewa, “Har yanzu muna da yakinin muna da gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi, wadanda babban nauyin da ke kansu shi ne kare rayuka da dukiyar kowane dan Najeroya ba tare da lura da kabila ko addini ko al’ada ko matsayi. Don haka wajibi ne gwamnatinmu ta kara zage dantse fiye da yadda take yi a yanzu don kare mana rayuka da kare kasarmu.”
kungiyar ta bukaci ’yan Najeriya su kasance a fadake kan babban hadarin da ke fuskantar “dukanmu da kasarmu a ciki da waje.”
Ta ce batun ba na wane ne zai zama shugaban kasa ko gwamna ko sanata bayan zaben 2015 ba ne, “Batu ne kan rayuwa da tsaro ga kowannenmu da ke son rayuwarsa kuma ya damu da zamanmu cikin lumana a matsayinmu na ’yan Najeriya,” inji sanarwar.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi