Limaman coci suna lalata da mata – Fafaroma
Fafaroma Francis ya amince cewa limaman coci-coci suna yin lalata da mata da ke hidima a majami’unsu kuma a wasu lokutan ma suna mayar da su tamkar bayi. Fafaroman ya yi tsokacin ne a lokacin da yake ziyara a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya ruwaito. Ya ce hakan ne ya […]
Fafaroma Francis ya amince cewa limaman coci-coci suna yin lalata da mata da ke hidima a majami’unsu kuma a wasu lokutan ma suna mayar da su tamkar bayi.
Fafaroman ya yi tsokacin ne a lokacin da yake ziyara a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
Ya ce hakan ne ya tilasta wa mutumin da ya gada, Fafaroma Benedict ya rufe wurin da malaman coci mata ke yin ibada saboda takwarorinsu maza na yin lalata da su.
Wannan ne karon farko da Fafaroma ya amince cewa limaman coci maza suna yin lalata da takwarorinsu mata da kuma hadiman coci.
Ya ce mahukuntan cocin suna kokarin magance matsalar amma “har yanzu tana ci gaba da faruwa.”
Fafaroma Francis ya yi wannan tsokaci ne ranar Talatar da ta gabata, a gaban manema labarai, lokacin da yake ziyarar a Gabas ta Tsakiya.
Ya amince cewa limaman coci da mataimakansu suna lalata da mata, kuma hukumomin cocin sun sani “amma suna aikin ganin an kawar da matsalar.”