Limaman cocin da aka gano ‘yaran sata’ fiye da 50 a Ondo sun shiga hannu

Tuni dai ’yan sanda suka tisa keyarsu zuwa hedkwatarsu don fadada bincike

Limaman cocin da aka gano ‘yaran sata’ fiye da 50 a Ondo sun shiga hannu

‘Yan Sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta kama limamin wani coci da mataimakansa da aka gano wasu kananan yara fiye da 50 da aka boye cikin wani wurin tsaro na karkashin kasa a cikin cocin.

Aminiya ta rawaito cewa an gano yaran ne wadanda ake kyautata zaton sato su a ka yi a ginin da ke cocin a unguwar Vanlentino a kwaryar birnin Jihar Ondo.

Kakakin rundunar a Jihar ta Ondo, Funmi Odunlami, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce za su yi cikakken bayani da zarar sun kammala bincike.

Bayanan da Aminiya ta tattaro daga wata majiya sun nuna cewa da yammacin Juma’ar da ta gabata ce ‘yan sandan suka yi dirar mikiya a wannan coci da ke unguwar ta Valentino a garin na Ondo inda suka ceto wadannan kananan yara maza da mata fiye da 50 da aka boye su cikin wani kebabben wurin tsaro na karkashin kasa a cikin cocin.

Bayan kubutar da yaran, ’yan sandan sun kwashe su tare da limamin cocin da ba a bayyana sunansa ba da wasu mataimakansa zuwa hedkwatar ‘yan sanda ta Jihar Ondo da ke garin Akure babban birnin Jihar domin ci gaba da bincike.