Limami ne ya sa na kashe mahaifiyata

Wata mata ta da yi wa mahaifiyarta kisan gilla ta ce wani limamin coci ne ya sa ta aikata. Matar mai shekara 30 ta ce ta yi amfani da adda ne ta fille kan mahaifiyarta  bayan da limamin cocin ya ce mahafiyar tata mayya ce. Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace Okorocha […]

Limami ne ya sa na kashe mahaifiyata

Wata mata ta da yi wa mahaifiyarta kisan gilla ta ce wani limamin coci ne ya sa ta aikata.

Matar mai shekara 30 ta ce ta yi amfani da adda ne ta fille kan mahaifiyarta  bayan da limamin cocin ya ce mahafiyar tata mayya ce.

Matar mai ’ya’ya hudu ta ce tana zargin mahaifiyarta ce ta sa mata ciwon tabin hankali.

“Na sare wuyanta ne da adda. Wani fasto ne ya ce mayya ce, shi ne na ji in roke ta. Mahaifiyata ’yar Jihar Enugu ce.”

Ta ce ta hallaka mahaifiyar tasa ce a lokacin da suke aiki a gona a unguwar Ile-Iluji.

A cewarta, “Wani abu ne ke damu na ya sa kashe mahaifiyata. Ban ji dadin abin da na aikata ba.”

Matar wadda aka gabatar tare da wasu wadanda ake zargi a Akure ta yi ikirarin cewa tana fama da tabin hankali.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ondo, Bolaji Salami, ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da matar a gaban kotu.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya