Limami ya kashe matarsa, ya boye gawar

’Yan sanda na bincike kan gawar matar, shi kuma ana tsare da shi.

Limami ya kashe matarsa, ya boye gawar

’Yan sanda a lokacin da suke bude ramin da wasu wadanda ake zargi suka jefa gawar matar da suka kashe. (Tsohon hoto).

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta cafke wani limami bisa zargin dukan matarsa har ta sheka lahira.

Kakakin Runduar, SP Odiko Macdon, ya shaida wa ’yan jarida a ranar Alhamis cewa an tono gawar matar da mijin nata wanda shi ne ya kafa wani coci, an kuma ajiye gawar a dakin ajiyar gawa don yin bincike.

  1. FGC Yauri: An kashe dan sanda, an sace malamai da dalibai
  2. Mahara sun kashe ’ya’yan manomi sun sace wasu

“Rundunar ta cafke wani mai shekara 49 mazaunin Karamar Hukumar Eket dan asalin Jihar Ebonyi kan zargin kashe matarsa tare da binne gawar a cikin wani rami da ke gidansa.

“Ranar 16 ga watan Yuni, 2021, da misalin karfe 2:00 na rana, wasu matasa suka kawo wa baturen ’yan sandan yankin Eket, CSP Sunday Digha, wanda ya kai cafke wanda ake zargin da kashe matarsamai shekara 40, uwar ’ya’ya biyar.

“Wanda ake zargin ya samu sabani ne da matar tasa, inda ya zarge ta da cin amana da jefa shi cikin matsaloli, wanda hakan yasa ya lakada mata dukan kawo wuka har ta mutu.

“Ya haka rami a gidan ya binne ta, amma ’yan sanda sun tono gawar sun kai ta dakin ajiye gawa domin a ci gaba da bincike,” inji shi.

Macdon ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zaran an kammala bincike.

Ya bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Amiengheme Andrew ya kadu da jin labarin, kuma ya bukaci ma’aurata su zama masu hakuri da warware matsalolinsu cikin salama.

Kwamishinan ya yaba wa matasan yankin bisa hadin kan da suka ba su, sannan ya gargadi masu aikata laifuka da su gujin hakan saboda rundunar ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin sun fuskanci hukunci.

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani