Limamin Bunza ya bukaci Musulmi su kyautata mu’amala a watan Ramadan

Babban Limamin Bunza da ke Jihar Kebbi Imam Hali Bunza, ya bukacii jama’ar Musulmi su tashi tsaye su nemi falalar da ke cikin watan Ramadan mai albarka ta hanyar kyautata mu’ala a tsakaninsu da yawaita karanta Alkur’ani Mai girma da aikata sauran ayyukan alheri. Sheikh Imam Hali Bunza ya ce, lokaci ya yi da Musulmi […]

Limamin Bunza ya bukaci Musulmi su kyautata mu’amala a watan Ramadan
Limamin Bunza ya bukaci Musulmi su kyautata mu’amala a watan Ramadan

Babban Limamin Bunza da ke Jihar Kebbi Imam Hali Bunza, ya bukacii jama’ar Musulmi su tashi tsaye su nemi falalar da ke cikin watan Ramadan mai albarka ta hanyar kyautata mu’ala a tsakaninsu da yawaita karanta Alkur’ani Mai girma da aikata sauran ayyukan alheri. Sheikh Imam Hali Bunza ya ce, lokaci ya yi da Musulmi za su daina zaman hira ba tare da yin aikin lada da zai sa da su da samun rahamar Allah a cikin wannan wata na tuba. Shehin malamin ya ce yin kiran ga Musulmi ya zama wajibi don su yi amfani da watan azumi wajen kaurace wa manya da kananan laifuffuka, kuma su yawaita tuba zuwa gare Shi domin Manzon Allah (SAW) ya ce a Hadisins shi kansa a rana yana tuba ga Mahaliccinsa sau saba’in, “Don haka wajibi ne ga Musulmi mu yi koyi mu rika yawan tuba zuwa ga Mahaliccinmu koyaushe,” inji shi. Babban Limamin ya ce, a cikin wannan wata akwai falala da garabasa na samun lada, kuma akwai wata kofa a gidan aljanna mai suna rayyan da babu wanda zai shige ta cikinta sai masu yin azumi, don ya kwadaitar da Musulmi su dage su nemi zama wadanda za su bi ta cikin wannan kofa ta Aljanna.