Limamin Ekiti ya zama Shugaban Majalisar Malaman Kurmi

A makon jiya ne aka nada Babban Limamin Ado Ekiti, Sheikh Jami’u Kewulere Bello a matsayin sabon Shugaban Majalisar Malaman jihohin Kudu maso Yamma da Edo da Delta.Malamin ya samu wannan mukami ce, bayan da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar  ya nada shi. A baya dai, Babban Limamin Oshogbo, Sheikh Ajisafe Mustafa […]

Limamin Ekiti ya zama Shugaban Majalisar Malaman Kurmi
Limamin Ekiti ya zama Shugaban Majalisar Malaman Kurmi

A makon jiya ne aka nada Babban Limamin Ado Ekiti, Sheikh Jami’u Kewulere Bello a matsayin sabon Shugaban Majalisar Malaman jihohin Kudu maso Yamma da Edo da Delta.
Malamin ya samu wannan mukami ce, bayan da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar  ya nada shi.
A baya dai, Babban Limamin Oshogbo, Sheikh Ajisafe Mustafa ne ke rike da mukamin, bayan da ya rasu ne aka ba marigayi Imam Suara na garin Ibadan rikon kwarya, wanda ya rasu kwanakin baya.
A duk jihohin Kudu maso Yamma, Jihar Ekiti ce mafi karancin Musulmi kuma wannan shi ne karon farko da jihar ta samu wannan mukami, wanda hakan ya sa masu fashin baki suka yi hasashen cewa adadin yawan Musulmin jihar ka iya karuwa, ta la’akari da tasirin wannan matsayi a addinance.
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ne ya jagoranci nadin  a Ado Ekiti, taron da masu ruwa da tsaki a sha’anin addinin Musulunci, musamman daga yankin Kurmi da sassa daban-daban na kasar nan suka halarta.
Sarkin Musulmi ya yi alwashin tabbatar da hadin kai a tsakanin al’ummar Musulmi, domin a cewarsa a yanzu al’ummar Musulmi na matukar bukatar hadin kai, ganin  irin  kalubalen da suke fuskanta. Ya kuma ce ba za su gajiya ba wajen shiga kowane bangare na kasar nan, a yunkurinsu na samar da hadin kai a tsakanin al’ummar Musulmi. Ya yi kira ga malamai su kara zage dantse wajen ba yara kyakkyawar tarbiyya saboda irin bacin sunan da ’yan ta’adda ke yi wa addinin Musulunci; inda ya ce ta’addancin ba ya da alaka da Musulunci, don haka za su yi iya kokarinsu wajen yakarsa ta hanyar yada  ilimi da fahimtar da jama’a cewa ta’addanci ba Musulunci ba ne.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Zikrullahi Muhammadu Al’awwal ya shaida wa Aminiya cewa wannan shugabanci da dan asalin jihar ya samu, za ta kara dankon zumunci tsakanin Musulmin  jihar da ’yan Arewa mazauna jihar, domin a cewarsa ’yan Arewa mazauna Ado Ekiti mutane ne masu son zaman lafiya da kiyaye doka.
Alhaji Abubakar Ahmad dan-Malamai, wanda shi ne Limamin Juma’a na farko a jihar a bangaren ’yan Arewa, ya shaida wa Aminiya cewa nadin Sheikh Jami’u Kewulere alheri ne gare su, domin shi mutum ne mai son jama’a kwarai da gaske.
Shugaban ’yan Arewa mazauna Jihar Ekiti, Alhaji Adamu Imam ya shaida wa Aminiya cewa sun yi murna kwarai da wannan baiwa da Allah Ya yi musu kana sun yi farin ciki da suka shaida ganin ziyarar Mai alfarma Sarkin Musulmi a jihar,  domin a cewarsa Sarkin Musulmi ne ba a Najeriya kadai ba, hatta ma ga daukacin Afirka ta Yamma don haka suka bar duk harkokinsu suka tare a inda suka yi masa masauki saboda su tabbatar da an ba shi kyakkyawar kulawa.