Limamin Juma’a Ya Yi Murabus Kan Kyautar Kuɗi

Ya zargi na’ibinsa da yi masa fince kan kuɗi Naira dubu ɗari biyar da gwamnan jihar ya bai wa kowane limami.

Limamin Juma’a Ya Yi Murabus Kan Kyautar Kuɗi

Babban Limamin Juma’a a masallacin Wala da ke Jihar Kebbi, Alhaji Rufai Ibrahim, ya ajiye mukaminsa na limanci a masallacin.

Alhaji Rufai Ibrahim dai ya yi murabus ne bayan da ya zargi na’ibinsa da yi masa fince kan kuɗi Naira dubu ɗari biyar da gwamnan jihar ya bai wa kowane limami.

Alhaji Rufai ya ce, na’ibinsa Malam Mamman Na Ta’ala Yahaya, ya ba shi Naira dubu ɗari biyu, maimakon ma su yi raba daidai.

Kwamishinan harkokin addinin Musulunci a Jihar Kebbi, Muhammed Sani, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, tuni dama Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kebbi ya dakatar da Imam Alhaji Ibrahim, kafin ya yi murabus daga mukaminsa na babban limami da raɗin kansa.

Aliyu ya ce murabus ɗin babban limamin ya samo asali ne daga rashin jituwa kan rabon wata kyauta ta Naira 500,000, inda ya yi zargin cewa na’ibinsa, Malam Mamman Na Ta’ala Yahaya, ya ba shi Naira 200,000 ne kawai daga ciki.

Ya kara da cewa, “maimakon Liman ya bayyana damuwarsa ta hanyar hukumar ma’aikatar kula da harkokin addini ta jiha, ko ta hukumar masarautu, ko kuma ga shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi, sai kawai limamin ya miƙa kokensa ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).”

Ya ci gaba da cewa, “Bayan dakatarwar da shugaban karamar hukumar ya yi masa, Liman Alhaji Ibrahim ya yanke shawarar yin murabus daga mukaminsa.

“Saboda haka gwamnati ta amince da murabus dinsa kuma ta umurci na’ibinsa da ya ci gaba da gudanar da harkokin masallacin.”

Kwamishinan ya buƙaci Majalisar Masarautar Gwandu da ke da alhakin naɗa sabon limami da ta gaggauta naɗa sabon babban limamin masallacin domin cike gurbin da Imam Alhaji Ibrahim ya bari.

 

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur