Limamin Masallacin ’Yan Majalisar Tarayya ya yaba wa Ndume

Limamin Masallacin Unguwar ’Yan Majalisar Dokoki ta kasa da ke Apo a Abuja Imam Ibrahim Awwal Usama Funtua ya yaba wa jama’a da kungiyoyin addini kan yadda suka rika kai masa ziyarar gaisuwa a lokacin da yake jinya a asibiti a makon jiya, inda ya ce, ya ji mamaki ganin mutanen da suka je duba […]

Limamin Masallacin ’Yan Majalisar Tarayya ya yaba wa Ndume
Limamin Masallacin ’Yan Majalisar Tarayya ya yaba wa Ndume

Limamin Masallacin Unguwar ’Yan Majalisar Dokoki ta kasa da ke Apo a Abuja Imam Ibrahim Awwal Usama Funtua ya yaba wa jama’a da kungiyoyin addini kan yadda suka rika kai masa ziyarar gaisuwa a lokacin da yake jinya a asibiti a makon jiya, inda ya ce, ya ji mamaki ganin mutanen da suka je duba shi.
 Imam Ibrahim Awwal ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce: “A gaskiya irin yadda na ga mutanen da ban yi tsammani ba, wadanda suka zo duba ni abin ya yi matukar ba ni mamaki. Don haka ina mika godiyata ga mutanen da suka ziyarce ni a asibitin musamman Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Mohammed Ali Ndume da tsohon Na’ibin Sufeto Janat na ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Bala Uba Ringim da Babban Jami’in Walwala na Jam’iyyar APC ta kasa Alhaji Ibrahim Masari da wakilan kungiyoyin Jama’atu Nasril Islam da Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da  da kungiyoyin agaji na JNI da na Izala da na Munazamatu Fityanul Islam da ’yan uwa da abokan arziki.”
Sanata Ali Ndume da ayarinsa sun ziyarci Imam Ibrahim Awwal a asibitin Primus International Super Speciality Hospital da ke Abuja. Sanata Ndume ya shaida wa limamin cewa sun je ne domin su gaishe shi bayan labarin da suka ji cewa yana jinyar a asibitin. “Mun yi wa Allah godiya ganin yadda muka zo muka tarar ka samu sauki. Kuma  muna rokon Allah Ya kara maka lafiya,” inji Sanatan.