Limamin sojoji ya bukaci a rika shiga bariki ana auren ’ya’yansu
Limamin Masallachin Juma’a na Barikin Soja na Bukabu da ke Kano, Kyaftin Hamisu Mustapha ya yi kira ga jama’ar gari su rika shiga barikin suna neman auren ’ya’yansu mata domin kulla zumunci a tsakaninsu da al’ummar gari.Kyaftin Mustapha ya yi kiran ne a lokacin bikin saukar karatun Alkur’ani na makarantar Islamiyya ta Fatima da ke […]
Limamin Masallachin Juma’a na Barikin Soja na Bukabu da ke Kano, Kyaftin Hamisu Mustapha ya yi kira ga jama’ar gari su rika shiga barikin suna neman auren ’ya’yansu mata domin kulla zumunci a tsakaninsu da al’ummar gari.
Kyaftin Mustapha ya yi kiran ne a lokacin bikin saukar karatun Alkur’ani na makarantar Islamiyya ta Fatima da ke barikin, inda ya ce, “Sau da dama mutanen gari suna tsoronmu kuma suna dari-darin neman ’ya’yanmu da aure saboda kallon da wasu ke yi wa mazauna bariki cewa suna aikata ayyukan masha’a. Amma yanzu kun ga yadda muke tarbiyyar ’ya’yanmu ta hanyar koya musu ilimin addini.”
Ya ce ka’idojin da ake bukata kafin daura auren shi ne gwajin jini na cutar kanjamau ga saurayi da budurwar da kuma yi wa mace awon ciki, don tabbatar da ba ta dauke da juna biyu.
A jawabin shugaban makarantar, Malam Ahmad Fagge ya ce an kafa makarantar ce a 1989 da dalibai 55 da ajujuwa biyu, amma yanzu makarantar tana da ajujuwa 7 da dalibai 1,300, kuma wannan ne karo na hudu na yaye daliban makarantar.
A jawabinsa, Limamin masallacin Gadon kaya, Dokta Abdullahi Umar Usman, ya yaba kan tarbiyya da kwazo da da’ar ’yan makarantar da ya ce ta dace da addinin Musulunci. Ya ce, “Da wani ne ya fada min irin tarbiyyar da yaran suke da ita da watakila sai na yi musu. Amma, alhamdulillah, na zo na gani da kaina.” Ya bukaci malamai da iyaye su ci gaba da ba ’ya’yansu ilimi mai amfani tare da kula da tarbiyyarsu.