Limamin Waje: Tinubu ya yi ta’aziyyar fitaccen limami a Kano
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar fitaccen mai wa’azin Musulunci a Jihar Kano kuma tsohon Wazirin Kano
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar fitaccen mai wa’azin Musulunci a Jihar Kano kuma tsohon Wazirin Kano, Sheikh Nasir Muhammad Nasir, wanda ya rasu yana da shekaru 87.
Shugaban kasa ya bayyana rasuwar fitaccen limamin a matsayin babban rashi, bisa la’akari da gudunmawarsa wajen kyautata rayuwar al’umma.
- Jirgin kasa ya kashe sojan Najeriya
- Gwamnan Sakkwato ya kafa kwamitin binciken gwanjon kayan gwamnati da Tambuwal ya yi
Sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, ya ce, “ Za a dade ana kewar Sheikh Nasir saboda yadda tafiyar da kusan da daukacin rayuwarsa wajen neman ilimi da yada shi da kuma yin wa’azi.
“Ba a Kano kadai ba, Najeriya ta yi rashin jajirtaccen malami wanda ba ya gajiya ko shakkar tsage wa shugabanni gaskiya.
“Ina rokon Allah Ya yi masa rahama, sannan ina mika ta’aziyya ga iyalansa da mabiyansa da kuma sarakunan Kano da Bichi da ma Gwamnatin Jihar Kano bisa wannan babban rashi,” in ji sakon na Shugaba Tinubu.