Liman ya gano amaryarsa namiji ne

An gufanar da wani matashi da ya yi shigar mata har wani limami ya aure shi a qasar Uganda. Matashin mai suna Swabullah Nabukeera ya riqa shigar mata har da hijabi ne yana zuwa masallaci inda wani limami mai suna  Muhammed Mutumba, mazaunin Kyampisi a Lardin Kayunga a qasar Uganda ya aure shi a matsayin […]

Liman ya gano amaryarsa namiji ne

Malam Muhammed Mutumba da ‘amaryarsa’ Richard Tumushave da ya ce sunansa Swabullah Nabukeera

An gufanar da wani matashi da ya yi shigar mata har wani limami ya aure shi a qasar Uganda. Matashin mai suna Swabullah Nabukeera ya riqa shigar mata har da hijabi ne yana zuwa masallaci inda wani limami mai suna  Muhammed Mutumba, mazaunin Kyampisi a Lardin Kayunga a qasar Uganda ya aure shi a matsayin mace.

Tuni aka dakatar da limamin, saboda ya auri namiji bisa tunanin mace ce, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito

Ma’auratan biyu ba su taba sanin juna a matsayin mace da miji ba, bayan da suka yi auren, inda ‘amaryar’ ta shaida wa angonta cewa tana jini al’ada, da ba zai ba su damar saduwa ba. Malam Mutumba, ya ce tunda matar tasa ta yi ikirarin tana jinin al’ada sai ya yi haquri da ita zuwa lokacin da za ta gama. Sai dai ‘amaryar’ da kullum ke cikin shigar mata ta yi nasarar haurowa ta katanga daga cikin gidan angonta bayan ta sace akwatun talabijin da kayan sawa, inda maqwabta suka suka kama ta.

Dubun ‘amaryar’ ta cika ce lokacin da ’yan sanda suke bincike kafin shigar da ita dakin tsare wadanda ake zargi da laifi, inda aka gano namiji ne sanye da hijabi da kayan mata. Bayan da ’yan sandan suka sanar da mijin sai ya kadu, inda ya nemi su ba shi dama ya tabbatar. Daga bisani dai wannan ‘amarya’ ta bayyana tabbas namiji ne kuma sunansa Richard Tumushabe, mai shekara 27, kuma ya auri limamin ne domin ya yi masa sata.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, angon ya ce ya hadu da shi ne a masallaci yayin da yake neman matar da zai aura.

“Na ci karo da wata kyakkyawar budurwa yayin da nake neman matar aure. Na nemi  aurenta kuma ta yarda, har ta ce ba zai yiwu mu sadu ba har sai na biya sadak an daura aure, inda na amince ta kai ni gidan gwaggwontaa qauyen Kituula. Kuma an daura aurenmu ne cikin mako daya da haduwarmu,” inji limamin.

’Yan sanda sun tsare amaryar da gwagonta bisa tuhumarsu da zamba cikin aminci kafin kai su kotu shekaranjiya Laraba, shi ma limamin aka dakatar da shi a masallacin da yake limanci, bisa zargin kauce wa koyarwar Musulunci wajne neman aure.