Limanci

Wani Bafulatani ne ya yi tafiya daga Arewa zuwa Kudu ci-rani sai suka yada zango wani kauye da Hausawa suka yi zango. Wurin ana sayar da abinci iri-iri har ma da wurin da aka kebe ana yin Sallah. Sai Bafulatanin nan ya sauke  kayansa, ya ga inda ’yan uwa suke ya huta, ya ci abinci. […]

Limanci
Limanci

Wani Bafulatani ne ya yi tafiya daga Arewa zuwa Kudu ci-rani sai suka yada zango wani kauye da Hausawa suka yi zango. Wurin ana sayar da abinci iri-iri har ma da wurin da aka kebe ana yin Sallah. Sai Bafulatanin nan ya sauke  kayansa, ya ga inda ’yan uwa suke ya huta, ya ci abinci. Bayan sun kammala, lokacin Sallah ya yi, sai ya tambayi ina masallaci yake, domin ya yi Sallah. Aka nuna masa. Da ma ya caba ado, ya yi shiga ta kamala, mutane suka yi alwala suka shiga masallaci. A ranar an yi rashin sa’a, limamin masallacin ya yi jinkiri bai zo a kan lokaci ba, sai aka ce wa wannan Bafulatanin: “Allah gafarta malam shiga gaba ka ba mu Sallah, don mun ga liman har yanzu bai zo ba; ga shi lokaci na neman kurewa.” Ashe ba su san cewa liman ya yi tafiya ba kuma na’ibi ma ba shi da lafiya. Bafulatanin nan ya zo ya ba da Sallah, bayan an gama sai mamu suka yabi liman, suka ce: “Ai kuwa wannan liman ya iya ba da Sallah!” Sai gogan naku ya juya ya kalle su ya fashe da dariya, ya ce: “Ai don ma ban yi Alwala ba, da kun ga wadda ta fi wannan.
Daga Aminu Auwal Kafinta, Kalaba 08068538118