Limanin Juma’a ya ajiye limanci don tsayawa takarar siyasa
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Masjid Umma da ke GRA a garin Katsina, Liman Muhammad Hashim, ya ajiye aiki domin tsayawa takarar siyasa. Liman Muhammad ya bayyana haka ne a wata takardar sanarwa mai dauke da hatimin masallacin, wadda ya rubuta ga kwamitin masallacin a ranar 24 ga watan Maris, 2022. NAJERIYA A YAU: ’Yan […]
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Masjid Umma da ke GRA a garin Katsina, Liman Muhammad Hashim, ya ajiye aiki domin tsayawa takarar siyasa.
Liman Muhammad ya bayyana haka ne a wata takardar sanarwa mai dauke da hatimin masallacin, wadda ya rubuta ga kwamitin masallacin a ranar 24 ga watan Maris, 2022.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan sandan da gaskiyarsu ta girgiza jama’a
- An kirkiro maganin kayyade iyali na maza
A cikin takardar da limamin ya kuma sanya wa hannu, ya bayyana cewa ya ajiye limancin ne saboda tsayawa takarar da zai yi, amma bai ambaci irin takarar da zai yi ba ko jam’iyar siyasar da zai fito a karkashinta inuwarta.
Amma hakan ya yi nuni da bin dokar zaben da ta ce duk wani mai rike da wani mukami na gwamnati ko kamfani da yake son tsayawa takara, lallai ne ya ajiye mukamin da yake rike da shi.
To sai dai abin da ake mamaki game da ajiye limanci da malamin ya yi shi ne, shin mukamin limanci yana daga cikin tsarin aikin gwamnati ko na kamfani, kuma me ya hada takarar siyasa da batun limancin masallaci?
Wasu kuma na ganin cewa, la’alla gwamnati ce ke biyan shi albashi a matsayin ma’aikaci da ke aiwatar da aikin limanci a masallacin da yake jagoranta.
Har dai zuwa rubuto wannan rahoto babu wani karin bayani da ya fito daga wajen Liman Muhammad ko kuma kwamitin da ke kula da masallacin da shi liman mai ritaya ya ba su haquri a kan wancan mataki da ya dauka.