Litinin da Talata ranakun hutun Babbar Sallah ne
Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun Litinin 13 da Talata 14 ga watan nan a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah.Ministan Al’amuran Cikin Gida, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba, a wata takarda da ta fito daga ofishin Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Muhammadu Maccido.Ministan ya roki al’ummar Musulmi da daukacin […]

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun Litinin 13 da Talata 14 ga watan nan a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah.
Ministan Al’amuran Cikin Gida, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba, a wata takarda da ta fito daga ofishin Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Muhammadu Maccido.
Ministan ya roki al’ummar Musulmi da daukacin ’yan Najeriy su karfafa kuma su ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya, a kokakinsa na bunkasa tattalin arzikin kasar nan, ta yadda za a samu ci gaba da yalwa cikin lokaci.
Janar Dambazau ya ce gwamnati tana sane da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, wanda ya faru sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya. Ya ce ana nan ana daukar matakan da suka dace na inganta al’amura, musamman a bangaren farfado da harkokin noma.