Littafi ko Fim: Wanne ya fi tasirin fadakarwa ga al’umma?
Littafi dai karanta shi ake yi, shi kuwa fim kallo ake yi kuma tare da sauraro. Wai tsakaninsu wanne ya fi tasirin fadakarwa da koyar da darussa ga al’umma? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suka fada: Littafi ya fi fim tasiri – Salisi Hapijo Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja Salisu Haladu […]
Littafi dai karanta shi ake yi, shi kuwa fim kallo ake yi kuma tare da sauraro. Wai tsakaninsu wanne ya fi tasirin fadakarwa da koyar da darussa ga al’umma? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suka fada:
Littafi ya fi fim tasiri – Salisi Hapijo
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Salisu Haladu Hapijo Galadinchi, Katsina: “Littafi ya fi fim amfani ga al’umma, musamman wajen isar da sako dalla-dalla kuma ya fi daraja wajen bayarwa kyauta don karramawa, sannan kuma ba ya saurin lalacewa, tunda ba sai ans a shi a na’ura ba.
“Amfanin fim sai da wutar lantarki kodayaushe amma littafi ko ba lantarki za a iya amfani da hasken safiya, rana ko kyandir da sauransu wajen karanta shi. Littafi ba ya saurin salwanta wajen adanawa. Hada fim yana da tsada kwarai, ba kamar buga littafi ba kuma sai an yi amfani da mutane da yawa a fim amma kalilan ne ke rubuta da wallafa littafi. Tun zamanin da ake amfani da littafi wajen jaddada tarihi da ilmi ga al’ummomi na ko’ina a duniya.”
Littafi ya fi fim fadakarwa – danladi Mai Neman Na Aure
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
danladi Mai Neman Na Aure dambatta: “A ganina littafi ya fi fadakarwa saboda shi littafi ya zagaya duniya kuma akwai shaharrarun mutane masu ilimin gaske, wadanda suka bautu wajan tsayawa su ga ya shiga lungu da sako don su ga ya fadakar da al’ummar duniya baki daya. Kuma shi littafi ko a makaranta ma ai ka ga da shi yara suke farawa wajan karuwar ilimi. To ka ga ai littafi yana sahun gaba wajan fadakarwa.”
Fim ya fi isar da sako da gaugawa – A’ishatu Ummi
Aliyu Babankarfi, a Zariya
A’ishatu Ummi B. Bashir, Tudun Wada Zariya: “A gaskiya fim ya fi littafi fadakarwa da wayar da al’umma da gaugwa fiye da littafi. Komai kuwa ba ya rasa dalili, domin yanzu idan marubuciya ta dage ta rubuta littafi, ba lallai ba ne ya isa ko’ina, birni da kauye kamar yadda fim ke zagayawa kuma ba kowa ke da ilimin karatu ba kuma idan da ilimin haka ba kowa ke jure karatu ba. Don haka fim yafi saukin wayarwa da kuma fadakar da al’umma a ganina.”
Ba a hada littafi da fim wajen tasiri – Aminu Labbo
Aminu A. Labbo Zariya: “Ba mahadi tsakanin littafi da fim, musamman irin wadannan fina-finan namu na zamani masu bata tarbiyya ta hanyoyi daban-daban, musamman ta wurin yanayin shigar da suke yi da kuma irin lafuzzan da suke fita a bakunansu. A don haka littafi ya fi, musamman littattafan da da na yanzu masu cike da hikima daban-daban. Don haka littafi ya fi fadakarwa da kuma wayar da kai fiye da fim, sai dai rashin zagayawa lunguna-lunguna kamar fim.”
Littafi ya fi gyara tarbiyya – Ibrahim Maiturare
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Alhaji Ibrahim Maiturare Da Atamfa: “Ra’ayina dangane da abin da ya fi gyara tarbiyyyar al’umma tsakanin littafi da fim shi ne, ai ko hadi babu littafi shi ne kan gaba wajen gyara tarbiyyar al’umma. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, shi littafi ai mai ilmi ne ke rubuta shi ko ma me ya kunsa ciki, sabanin fim wanda duk wadda aka dora shi kan layinsa zai iya yi ba tare da wata wahala ba.
“don haka littafi shi ne kan gaba sabanin fim wadda rashin amfaninsa ya fi amfaninsa yawa kasancewar ko a halin da ake ciki ma akasari mafi yawansu su ke kan gaba wajen gurbata tarbiyyar matasanmu daga bangaren mata da maza, musamman wajen koyar da rashin kunya da rashin girmama na gaba da uwa ubansu koyar da sa kayayyaki na tsiraici.”
A addinance littafi ya fi fim – Ado Ibrahim Kwaya
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Ado Ibrahim Kwaya Mai hoto: “Ra’ayina dangane da wanda ya fi muhimmanci wajen gyara tarbiyyar al’umma tsakanin littafi da fim, ai da gani babu tambaya. In dai maganar gyara tarbiyya ne, musamman ga mu al’ummar Arewacin kasar nan, wadanda aksarinmu masu addini ne, littafi shi ya fi fa’ida. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, shi littafi ai abu ne da kake karanta shi kuma in kana karanta shi za ka ga tamkar kana kallon abin da ya kunsa ne kuma in ka karanta shi za ka tarbiyyantu tare kuma da adana shi domin gaba a matsayin tarihi.
“To amma shi fim koda ya fadakar ma to daga bisani kuma za ka iya ganin munanan halayen da kan iya gurbata tarbiyya, musamman ta wajen furta kalamai marasa tarbiyya ciki da kuma sa suturun da suka yi hannun riga da irin wadanda addininmu da al’adunmu suke yin hani da su.”