Littafin Awa Ashirin Da Hudu A Gidan Dabo a mahangar nazari

Sunan Littafi: Awa Ashirin Da Hudu A Gidan DaboSunan Marubuciya: Rabi’a Talle MaifataKamfanin dab’i: Edpert Printers, KanoShekarar Wallafa: 2014Yawan Shafuka: 112Farashi: N500 Tarihi babbar taska ce mai dauke da gagarumar gudunmowa ga al’umma. Da tarihi ne ake duba jiya domin sassaita tafiyar yau tare da hango ko tsinkayo gobe.La’akari da kalamin da ya gabata, samun […]

Littafin Awa Ashirin Da Hudu A Gidan Dabo a mahangar nazari
Littafin Awa Ashirin Da Hudu A Gidan Dabo a mahangar nazari

Sunan Littafi: Awa Ashirin Da Hudu A Gidan Dabo
Sunan Marubuciya: Rabi’a Talle Maifata
Kamfanin dab’i: Edpert Printers, Kano
Shekarar Wallafa: 2014
Yawan Shafuka: 112
Farashi: N500

Tarihi babbar taska ce mai dauke da gagarumar gudunmowa ga al’umma. Da tarihi ne ake duba jiya domin sassaita tafiyar yau tare da hango ko tsinkayo gobe.
La’akari da kalamin da ya gabata, samun tarihin muzakkarin shugaba, sarki, malami irin mai martaba marigayi Alhaji (Dokta) Ado Abdullahi Bayero, babban jari ne ga al’ummar yau da kuma mai zuwa nan gaba. Bisa ga haka, littafin nan da muke nazari a yau, ya kasance wani mabudin ilimi, jagora ga shugabanni mai dauke da babbar taska ga al’umma da ya shafi mulki, al’ada, addini da kuma wayewar zamani.
Kamar yadda mashahurin malamin adabi ya bayyana, a lokacin da yake kattaba gabatarwa ga littafin, Farfesa Ibrahim Malumfashi yana cewa: “Awa 24 A Gidan Dabo, littafi ne da ya kawo mana hoton rayuwar Sarkin Kano, Ado Bayero daga tashi barci zuwa kwanciya, inda aka tattauna yadda sarki ke cin abincin safe da yadda yake fita zuwa ofis, daga nan sai ya dawo cikin gida ya yi shirin fita fada. A nan an kawo mana yadda Sarki ke karbar gaisuwa daga jama’ar gida da suka hada da mata da ’ya’ya da kwara-kwarai da sauran al’ummar gari. An kuma bayyana rayuwar Sarki kafin shiga fada da kuma yadda tsarin fadar take a halin yanzu.” (shafi na id).
Littafin bai tsaya kan rayuwar Sarki Ado kadai ba, sai da ya koma baya ya bayar da tarihin Kano da sunayen sarakunan da suka mulke ta tun daga shekarar 999 zuwa kan Ado (2014). An yi bayanin mulkin Fulani da yadda jihadi ya kasance a Kano. An yi bincike game da yadda sarauta ta samu a Gidan Ibrahim Dabo, wanda shi ne tushen Sarko Ado da aka tsira littafin nan kan rayuwarsa.
A sauran kunshiyar littafin, marubuciyar ta yi bayani dalla-dalla game da rayuwar San Kano Ado Bayero, haihuwarsa, kuruciyarsa, iliminsa, ayyukansa kafin sarauta, yadda aka zabe shi da nada shi sarautar Kano da kuma irin girmamawar da ake yi masa a gida da waje. An yi bayani game da ayyukan bunkasa kasa a zamaninsa da bayani game da kasashen duniya da ya ziyarta.
Kasancewar an yi zuzzurfan bincike kafin a rubuta littafin, an yi bayani game da ma’anar wasu kalmomi da suka shafi mulkin gargajiya, kamar kalmar ‘hakimi’ da sauransu. An kawo jerin sunayen hakiman sarkin Kano, sunayen sarautun da ake ba ’ya’yan sarki, sarautun mataimaka sarki, sarautun masu ilimi, sunayen hakiman da sarki Ado ya tarar a kan mulki, sannan kuma aka zayyana jerin sunayen hakiman masarautar Kano a 2013.
Dayake littafin kambamau ne game da masarautar Kano, marubuciyar ta yi bayani game da bunkasar Kano a zamanin mulkin Sarki Ado, wadanda suka hada da yada addinin Musulunci, samar da zaman lafiya tsakanin sarakuna biyu a Kudancin Najeriya, samar da zaman lafiya a tsakanin Kiristoci mazauna Kano.
Daga shafi na 31 zuwa na 53, marubuciyar ta karkato da bayani game da mata da ’ya’yan Sarki Ado Bayero da kwara-kwaransa, sannan ta kawo dukkan sunayen ’ya’yan sarkin, maza da mata. Ta yi bayani game da yanayin Gidan Sarautar Kano a yau da kuma shugabanci da tsarin zamantakewa a gidan. Bayani ya gabata game da mukaman Mai Babban dai da Uwar Soro da Mai Soron Baki da Uwar Waje da Mai Kudandan da Kuyangi da Jakadu.
Daga shafi na 54 zuwa 74, littafin ya karkata zuwa wasu bayanai da suka hada da harshen magana a Gidan Sarautar Kano, fadojin gidan sarki da sunayen ranakun da yake zama a cikinsu. Akwai bayanin yadda Magajin Dabo yake kasancewa a Gidan Rumfa – bayanan da suka hada da tashinsa daga barci, alwala da Sallar Asuba, karya kumallo, fita ofis, shirin fita fada da suturar da mai martaba ke sakawa da suka hada da takalmansa, yadda yake komawa cikin gida, yadda yake fita zuwa masallaci, yadda yake cin abincin rana, yadda yake yin sadaka da kuma yadda yake yin barcin kailula.
Sauran bayanan da littafin ya kawo daga shafi na 74 sun hada da yadda sarki ke kasancewa bayan Sallar Isha’i da wasu salloli da yake yi. Akwai bayani game da bukukuwan da ake gabatarwa na Sallar Idi da sauransu, sannan kuma littafin ya karkaye da jawabin kammalawa, wanda ya yi tariyar kunshiyar littafin gaba daya.
Wasu abubuwan lura da jan hankali game da littafin:
Marubuciyar littafin ba ta yi kyuya ba, domin kuwa ta dora aikinta bisa mizanin bincike. A duk bayanan da ta kattaba, takan kafa hujja mai kwari da madogarar da ta samo bayanin. Kamar yadda Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce: “Wannan littafi ya bibiyi yadda fasalin gidan sarki yake da kuma masu hidindimun gidan a kowace rana ta Allah. Abin burgewa daga wannan aikin littafi, shi ne, wasu abubuwan da ke ciki ganau ne ba jiyau ba.
“Na tabbata wannan littafi zai bayar da gudunmuwa wajen tanadar da wani bangare na rayuwar Sarautar Kano da sarkin Kano Ado Bayero a daidai lokacin da sarki ke cika shekara 50 a bisa karagar Sarautar Kano. Littafi ne da zai zama abin tunkaho ga masu nazarin tarihi da siyasa da mulki da adabi da al’adu da kuma zamantakewa, ba kawai ta kasar Kano ba, har da sauran sassan kasar Hausa.” (Shafi na id zuwa d).
Littafin nan, a shafi na 14 zuwa 15, ya bayyana yadda Turawan Mishan suka yi wa Musulunci barna saboda soke aiki da Shari’ar Musulunci. “Lambar girmamawa ta J.P (Justice of Peace), wadda Gwamnatin Jihar Kano ta ba shi, sakamakon soke gudanar da Shari’ar Musulunci da aka yi, inda ya zama mai sulhu ga mutane.”
Haka kuma, batun bayi, sadaku da kwara-kwarai a Masarautar Kano da aka yi a shafi na 50, shin hakan yana nuna cewa har yanzu ana yin bauta? Wannan kalubale ne ga masu kare hakkin dan Adam da su san yadda za su dakile wannan al’ada, domin kuwa wannan zamani ne na ’yanci.
A shafi na 61, littafin ya bayyana yadda marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ke bin jam’in Salla daga gida, shi kadai. “Ba ya fita masallacin, a cikin gida yake bin jam’i. Akwai amsa kuwwa da aka janyo ta tun daga masallacin har sararin Garke aka mammakala su jikin rumfar kasa da kusurwowin da suke sararin Garke.”
Allah Shi gafarta wa sarki, wannan ya nuna cewa ya kamata malaman Musulunci su san yadda za su yi wa sarakunanmu nasiha, su gane cewa a matsayinsu na magada Shehu Usman danfodiyo, ba ya kamata su rika bin jam’in Salla daga gida, domin kuwa ba haka Musulunci ya tabadar ba. Yin hakan kuma ba kamala ba ce, nakasu ne a gare su.
Duk da cewa littafin nan ya rubutu, wanda haka ya sanya kura-kuran dab’i suka yi karanci a cikinsa, an samu tuntuben na’ura a wasu wuraren daban-daban. Haka kuma akwai wasu hotuna masu muhimmanci da ak yi amfani da su a shafi na 75 zuwa 77, amma suka fito a dusashe. Ya dace a ce sun fito radau, domin kuwa muhimmancinsu a littafin ba kadan ba ne.   
Haka kuma, a rayuwar sarki Ado, ya samu sabani da rashin jituwa da wasu gwamnoni, musamman ma marigayi Abubakar Rimi da kuma gwamna mai ci a yanzu, Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya dace a ce marubuciyar ta yi bincike ta bayyana irin wadannan rashin jituwa da suka faru da kuma yadda aka samu sulhu da sasanci a tsakani. Wannan zai kara inganta littafin kuma ya bar darasi abin koyi ga shugabanni.
Haka kuma, akwai bayanai masu karfi da ke bayyana marigayi Sarkin Kano da cewa attajiri ne sosai, domin kuwa kafin rasuwarsa ya kasance mai kokari wajen sana’a da kasuwanci. Ya dace a ce an yi bincike an bayyana dalla-dallar haka a littafin nan, domin kuwa wannan misali ne mai kyau, abin koyi ga wasu shugabanni da malamai da suke nade hannu su zama cima-zaune.
Kamar yadda Nasiru Wada Khalil ya ce: “Littafin Awa Ashirin Da Hudu Na Sarkin Kano shi ne littafi na farko tun da aka kafa Masarautar Kano fiye da shekaru 1000 da doriya, da ya kalli rayuwa ta shugaba a kankin kansa kuma ya yi nazarinsa ta yadda zai amfani al’umma. Wannan littafi ya koyar da yadda ya kamata mutum ya shugabanci iyalinsa da yadda zai jibinci lamarin iyalinsa komai irin nauyin shugabancin da yake a kansa. Wannan marubuciya, Rabi’a Talle ta bude wata kofa ta ilimi, musamman ga masana dabi’u da zamantakewar dan Adam, masu kare hakkin mata da kimiyyar shugabanci da sauransu.”
 Babu shakka littafin nan ya bijiro da kafar nazari mai girma ga al’umma, don haka ya dace cibiyoyin ilimi, tarihi, adabi, al’adu da daidaikun mutane su mallake shi.