Littafin Bayanin Hukuncin Zalunci

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.Babi na Farko:Bayanin zalunci da kwace. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ka yi tsammani Allah Yana Mai shagala daga abin da azzalumai suke aikatawa. Abin sani kawai, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani yini, wanda idanuwa suke fita tsuru-tsuru (manya-manya) a cikinsa. Suna masu gaggawa, masu daukaka […]

Littafin Bayanin Hukuncin Zalunci
Littafin Bayanin Hukuncin Zalunci

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Babi na Farko:
Bayanin zalunci da kwace. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ka yi tsammani Allah Yana Mai shagala daga abin da azzalumai suke aikatawa. Abin sani kawai, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani yini, wanda idanuwa suke fita tsuru-tsuru (manya-manya) a cikinsa. Suna masu gaggawa, masu daukaka kawunansu zuwa sama, kiftawar ganinsu ba ta komawa gare su. Kuma zukatansu wofintattu (ba su da hankula). Kuma ka yi gargadi ga mutane ga ranar da azaba take je musu, sai wadanda suka yi zalunci su ce, “Ya Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karba wa kiranka, kuma mu bi Manzanni. (Allah Ya ce musu) “Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwa ba daga gabani, cewa ba ku da wata gushewa? Kuma kuka zauna a cikin gidajen wadanda suka zalunci kawunansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikata game da su, kuma Muka buga muku misalai. Kuma lallai sun yi makirci irin makircinsu, kuma a wurin Allah makircinsu yake, kuma lallai ne makircinsu ya kasance, hakika, duwatsu suna gushewa saboda su. Saboda haka, kada ka karfafa zaton Allah Mai saba wa wa’adinsa ne ga Manzanninsa. Lallai ne, Allah ne Mabuwayi, Ma’abucin azabar ramuwa (k:14:42-47).”

Babi na Biyu: Ramuwar Zalunci:
160. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Mu’azu dan Hisham ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari daga kattada daga Abu Mutawwakil. Na ji daga Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi) daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan muminai suka tsira daga wuta sai a tsare su a wata kadarko (gada) tsakanin wuta da Aljanna, a yi musu hukunci da abin da yake na zalunci da ya kasance tsakaninsu a duniya har a tsarer da su a tarbiyyantar da su. Sa’an nan a yi musu izini da shiga Aljanna. (Annabi SAW) ya ce: “Ina rantsuwa da Wanda ran Muhammad (SAW) yake hannunSa mutum zai fahimci gidansa na Aljanna fiye da yadda zai fahimci gidansa na duniya.” Yunus dan Muhammad ya ce, Shaiban ya ba mu labari daga kattada ya ce, Abu Mutawwakil ya ba mu labari (da shi).

Babi na Uku:
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku saurara! La’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai (k:11:18).”
161. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba ni labari daga Safawan dan Muhriz Mazini ya ce: “Wata rana ina tafiya tare da dan Umar (Allah Ya yarda da su), yana rike da hannunsa sai wani mutum ya gitta (bayyana) ya ce: “Kamar yaya ka ji Manzon Allah (SAW) ya ambaci yadda ganawar mutum da Allah za ta kasance Ranar kiyama? Ya ce, “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Hakika Allah zai kusanto da mumini sai ya sanya shamaki ya suturce shi, Yana cewa: “Shin ka san wannan zunubi kaza? Shin ka san zunubi kaza? Sai ya rika cewa: “Na’am, ya Ubangiji har ya yi Ikirari da zunubinsa ya ga kansa shi dai ya halaka.” (Sai Allah) Ya ce: “Na boye su gare ka a duniya, a yau kuma na gafarta maka, sai a ba shi littafin kyawawan ayyukansa. Amma kafiri da munafiki sai ayyukansu su yi musu shaida cewa: “Wadannan su ne suka karyata bisa ga Ubangijinsu. Ku saurara! La’anar Allah ta tabbata ga mutane azzalumai (k:11:18).”