Littafin Falsafar Bukar Usman: Rayuwar Hadimin Al’umma a shekara 77
Sunan Littafi: Falsafar Bukar Usman. Sunan Marubuci: Khalid Imam. Kamfanin Wallafa: Whetstone Publishers, Kano. Yawan Shafuka: 266. Shekarar Wallafa: 2019. Farashi: Ba a fada ba. A ranar Talatar da ta gabata ce Dokta Bukar Usman (OON), marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Kasa ya cika shekara 77 a duniya. Kuma a cikin wannan wata […]
Sunan Littafi: Falsafar Bukar Usman.
Sunan Marubuci: Khalid Imam.
Kamfanin Wallafa: Whetstone Publishers, Kano.
Yawan Shafuka: 266.
Shekarar Wallafa: 2019.
Farashi: Ba a fada ba.
A ranar Talatar da ta gabata ce Dokta Bukar Usman (OON), marubuci kuma tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Kasa ya cika shekara 77 a duniya. Kuma a cikin wannan wata ne wannan littafi da muke wa sharhi a yau ya bayyana. Littafi ne da ya tattara bayyanan tarihi, halaye da dabi’un Bukar Usman, kamar yadda mawakan zamani suka zayyana a mabambantan wakokinsu. Haka kuma yana kunshe da bayanan zahiri na tarihinsa da ayyukansa da wallafe-walllafensa, kai har ma da bayani cikkake game da gidauniyarsa, wacce ya kafa da nufin taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban na rayuwa-Gidauniyar Bukar Usman.
Littafin nan, an kasa shi zuwa sassa biyar, inda kashi na farko ya faro daga shafi na 5 zuwa na 38 kuma ya kunshi Sadaukarwa, Godiya, Takaitaccen Tarihin Mawallafi, Takaitaccen Tarihin Dokta Bukar Usman da Takaitaccen Tarihin Gidauniyar Dokta Bukar Usman. Haka kuma akwai Gabatarwa da Ta’aliki da kuma Sharhi.
A kashi na biyu, wanda ya faro daga shafi na 39, ya kare a shafi na 130, yana kunshe ne da gundarin (matanonin) wakoki 14 da mabambantan mawakan zamani suka yi wa Dokta Bukar Usman. Wadannan wakoki kuwa sun hada da Jarumi, Gwanin Kowa, Doktan Adabi, Falsafar Bukar Usman, Farfesa Ya Zo Ya Gaishe Ka, Garnakaki da Ginshikin Adabi. Sauran sun hada da, Bai Rike Mu Da Wasa Ba, Kana Da Ilimi Ga Girma, Madugu Uban Tafiya, Sha Gwagwarmaya, Mai Kishin Biu da kuma Ilimi Abin So Ne.
A kashi na biyu kuwa, wanda ya faro daga shafi na 131 zuwa 144, ya kunshi Wakokin Gidauniyar Dokta Bukar Usman ce. Wakoki biyu ne aka zayyano, wadanda suka hada da mai taken Gidauniyar Ceto da kuma Gidauniyar Taimakon Al’umma.
Kashi na uku na littafin kuwa, yana kunshe ne da Wakokin Kasar Biu da na Borno. Wannan kuwa ya faro daga shafi na 145 zuwa na 218. A cikinsa ne aka jero matanonin wakoki masu take kamar haka: Garin Biu, Mu Gyara Kasar Biu, Matasan Biu da Alhaji Mai Umar Mustapha, Sarkin Biu. Akwai kuma wakoki masu taken: Mu Hada Kanmu ’Yan Borno, Gaskiya Ta Yi Halinta da kuma Mun Yaba Mun Gode.
Idan muka tuntuda zuwa Kashi na Hudu na littafin kuwa, za mu iske Takaitaccen Tarihin Mawakan da suka samar da katafanin wakokin littafin. Wannan kashi kuwa ya faro ne daga shafi na 219, ya karkare a shafi na 226. Mawakan da aka tattauna batutuwansu kuwa sun hada da Aminu Ladan Abubakar (ALA) da Maryam A. Baba (Sangandale) da Sulaiman A. Tijjani (Farfesan Waka) da kuma Umar Idris (Dankwairon Biu).
Sai kuma Kashi na Biyar, duk da cewa marubucin littafin bai kira shi da kashi ba, amma dai ya faro daga shafi na 227 zuwa 266. A wannan bangare ne aka gabatar da Ma’anonin Wasu Kalmomi da suka bayyana a littafin. Sannan kuma aka karkare da Matashiya ko kuma Rataye, kamar yadda ake kiransu a tsarin wallafa.
A iya sanina da littattafan Hausa, wannan littafi na Falsafar Bukar Usman, shi ne irinsa na farko da aka taba wallafawa a duniyar Hausa. Me ya sa na ce haka? A can baya, an samu marubuta sun yi rubutu game da mawakan baka da wakokinsu, an samar da littattafai game da marigayi Danmaraya Jos, an samar game da marigayi Mamman Shata, an samar a kan marigayi Narambada da sauransu, amma ban taba ganin littafi da ya tattara wakokin da mabambantan mawaka suka yi wa mutum daya ba sai wannan.
Waka a al’adar Bahaushe na daya daga cikin hanyoyin nishadi, fadakarwa, nunarwa, haka kuma hanya ce ta adana tarihi. Don haka a wannan kundi, wanda ke kunshe da wakoki mabambanta, sun ta’allaka ne a kan wadannan maudu’ai da na lissafa. Mawakan Hausa kan dauki wani abu ko wani mutum su wake shi, ko dai su kambama shi, ko su bayyana alherinsa, ko su kushe shi ta hanyar yayata sharrinsa. A iya nazarin da na yi wa dukkan wakokin da ke kunshe a littafin nan, jigonsu da hanyarsu daya ce – bayyana halaye, manufofi, ayyuka da siffofin Dokta Bukar Usman OON, da mahaifarsa da jiharsa da kuma mutanen da ke tattare da shi, kamar Sarkin Biu da sauransu.
Wani abu da ya kara wa littafin armashi shi ne, yadda aka kawo tarihin shi Dokta Bukar, sannan aka kawo bayani dalla-dalla na gidauniyarsa da ya kafa, wacce ta ta’allaka ga taimakon al’umma. Mai karatu ko mai nazarin littafin, cikin sauki zai iya kwatanta kalaman mawakan da kuma rayuwar wanda aka wake, inda zai samu sakamakon da yake bukata. Nan zai tantance gaskiya ko akasin kalaman mawakan dangane da wanda suka yi wa wakar, sha yanzu kuma magani yanzu.
Haka kuma, bayan matanonin wakokin da aka zayyano, marubucin littafin kuma ya yi kokarin tattaro takaitattun tarihin mawakan gaba daya, inda hakan zai ba mai nazarin littafin bayanai da siffofinsu. Haka kuma, mutum zai gane kima da darajarsu a duniyar mawakan Hausa. Ta haka ne za a gane fassarar salon maganar nan ta Hausawa da ke cewa, babban goro sai magogin karfe. Ma’ana, idan aka ce fitaccen mawaki irin ALA ya yi wa mutum waka, lallai hakan ke nuna matsayi da kimarsa.
Shin me malaman Hausa suka ce game da wannan littafi? Ga abin da Farfesa Aminu Lawan Auta, Malami a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Bayero Kano ya ce, a shafi na 34 na littafin: “Hakika wannan littafi ya zo a kan kari, domin zai zama jari ga masu yunkurin nutso cikin kogin nazarin adabi tare da samar da farfajiya ga mai karatu tare da warware wasu kalaman da ba a iya fahimta ba a wakokin da aka rera cikin faifan sidi (CD). Ina fata duk wanda ya samu mallakar wannan littafi zai rike shi kuma ya yi amfani da shi yadda ya kamata.”
Ba wannan kadai ne ba, ga wani batun kuma: “Wannan littafi da aka ba wa suna Falsafar Bukar Usman: Kundin Wakokin Hausa na Zamani, littafi ne da ya kunshi jerin wasu wakoki na Hausa na zamani da aka yi wa wannan shahararren masani, gogagge kuma tsohon ma’aikaci, wanda ya yi fice a matsayinsa na marubucin adabin baka; musamman tatsuniyoyi da al’adu da tarihi da mulki da gudanarwa da kuma harkar tsaro da dai sauransu. Sunan da aka ba wa wannan littafi ya dace kwarai, duba da irin tarin falsafar da ke tattare da rubuce-rubucen Dokta Bukar.” Abin da Dokta Halima Abdulkadir Dangambo, Malama a Sashin Koyar da Harsunan Najeriya, a Jami’ar Bayero Kano ta bayyana ke nan a ta’alikinta ga littafin, a shafi na 35.
Wane ne Bukar Usman a fuskar Umar Idris (Dankwairon Biu)? Mawakin a shafi na 41, yana cewa: “Yau ga Dankwairon Biu, Umar Idrisa a zahiri. Dokta Bukar Usman Biu, Umar ni na san da kai. A zahiri fa kai ba ka san ni ba. Ya zan dole na san da kai. Tun da kai ka rubuta a san da kai. Ya Allahu Ubangiji, Ya raba ka da sharrin duniya, Ya raba ka da tashin hankali. Dokta Bukar Usman Biu, kana da taimako fa ta ko’ina. A kasar nan duk an san da kai. Baba da ku aka damawa gida, kuma da ku aka damawa waje.”
Shi kuwa Suleiman A. Tijjani (Farfesan Waka), cewa ya yi a wakarsa da ta fito a shafi na 58 na littafin: “Ga mai falsafa abin koyi. Ga mai falsafa ta alfarma. Dokta Bukar yana da alheri. Dokta Bukar yana da alfarma. Dokta Bukar yana da alfarma.”
Shi kuwa Abubakar Ladan Abubakar (ALA), a tasa wakar ga Dokta Bukar, wacce ta fito a shafi na 86 na littafin, yana cewa: “Wani ya yi rankatakaf ga sani ga kwabo da dari. Kana fagen hikimia manihi ne gwanin shi’iri. A fagen mu’amilla a nan a kai masa shan sukari. Dokta Bukar na Biu mai hali tarra duk nagari.”
Game da Gidauniyar Bukar Usman kuwa, Zabaya Maryam A. Baba (Sangandale), a wakarta da ta fito a shafi na 139 na littafin, tana cewa: “Gidauniyar Bukar Usmanu taimakon al’umma ne. Gidauniyar Bukar Usmanu raya al’umma ne. Gidauniyar Bukar Usmanu ginshikin tofo ne. Gidauniyar Bukar Usmanu tattalin ilimi ne.”
Babu shakka, wannan littafi wani kandami ne da ya tanadar da wurin da masana da manazarta za su yi iyo domin fitar da ilimi ga al’umma. Haka kuma bagire ne da aka dibiya fasaha da fikira, rumbu ne da aka adana da alkinta adabin Hausa. Littafi ne da aka natsu aka samar da shi, tare da inganta wallafarsa, musamman ta hanyar bin dukkan wasu ka’idoji da tanade-tanaden wallafa na duniya. Ga shi dai an tsara shi da zayyanar bango mai daukar hankali, sannan an yi taka-tsan-tsan wajen kauce wa kura-kuran dab’i, duk da cewa wasu sun bayyana, amma ba su taka kara suka karya ba.
Idan har akwai wani abu da za a ce ya kamata a yi a littafin nan, wanda kuma ba a yi ba, shi ne: Ya kamata a ce marubucin littafin nan ya fadada aikinsa, ya zabi wasu daga cikin manyan wakokin nan ya biyo bayansu da sharhi da fashin baki. Lallai kam da aikin ya kara armashi. Kodayake, wannan kuma ta zama sabuwar kofa ga manazarta da za su maida hankali a wannan fannin.
Aiki dai kam ya yi, saura da me, ya kamata al’umma daidaiku da cibiyoyin ilimi su mallaki littafin nan, domin kuwa rumbu ne na ilimi, ingizau ne mai tunzura al’umma su aikata alheri, kamar dai yadda mawakan nan suka fito da halayen Dokta Bukar Usman Biu, a sakamakon ayyukansa na alheri ga al’umma.