Littafin Jagoran aikin hajji a ma’aunin nazari

Sunan Littafi: Jagoran Aikin HajjiWallafa: Hukumar Alhazai ta Jihar Kano Shafuka: 94 Bugawa: Kamfanin Baba Printers Babu shakka littafin da Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Kano ta wallafa mai suna Jagoran Aikin Hajji ya amsa sunansa idan aka yi la’akari da yadda aka tsara shi da kuma irin zurfin binciken da aka yi a […]

Littafin Jagoran aikin hajji a ma’aunin nazari
Littafin Jagoran aikin hajji a ma’aunin nazari

Sunan Littafi: Jagoran Aikin Hajji
Wallafa: Hukumar Alhazai ta Jihar Kano Shafuka: 94 Bugawa: Kamfanin Baba Printers

Babu shakka littafin da Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Kano ta wallafa mai suna Jagoran Aikin Hajji ya amsa sunansa idan aka yi la’akari da yadda aka tsara shi da kuma irin zurfin binciken da aka yi a kan aikin Hajji tare da tace sakonnin da littafin yake isarwr ga maniyyaci.
Idan muka yi nazari sosai, za mu ga cewa jigon littafin ya dace da sunan da aka rada masa kuma sakon da ake so a isar ga maniyyaci babu shakka zai kai gare shi ba tare da wata matsala ba cikin sauki.
Bisa la’akari da zubi da tsarin littafin, gaskiya an yi yadda ya dace musamman ma irin yadda aka tsara abubuwan da ke cikin littafin bi-da-bi, daya-bayan-daya, ba tare da hautsuna su ba. An tsara littafin fasali-fasali tun daga fasali na daya har zuwa fasali na takwas, inda aka yi maganganu a kan muhimmancin aikin Hajji da nisihohi ga maniyyata da shirye-shiryen tashi da aikin Hajji da batun Mikati da Safa-da-Marwa da dawafi da Jifa da Hawan Arfa da sauransu.
Haka ma sanya batun wuraren ziyara da tambayoyi da amsoshi saboda maniyyata da fadakarwa kan Hukumar Aikin Hajji Ta kasa da Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Kano da batun tanade-tanaden Hukumar Saudiyya ga maniyyata da shirye-shiryen komawa Jidda da kuma shirye-shiryen komawa gida Najeriya. Duk wadannan batutuwa ne da za su wayar wa da maniyyaci kai, ta yadda zai yi aikin Hajjinsa ba tare da wata matsala ba.
Duk da cewa an yi kokari kwarai da gaske wajen bin ka’idar rubutu da kuma yin amfani da daidaitacciyar Hausa, an dan sami kura-kurai a wasu wuraren, inda aka rika yin kuskuren hada wasu kalmomi da a ka’ida raba su ake yi. Kamar a shafi na biyar an hade kalmar ‘yazo’ a maimakon ‘ya zo’ da kalmar ‘hanasu’ a maimakon ‘hana su’ da kalmar ‘akan’ a maimakon ‘a kan.’ Sai a shafi na tara inda aka rika hade kalmar ‘zaka’ a maimakon ‘za ka.’ Hakazalika a shafi na 36 an hade kalmar ‘sune’ a maimakon ‘su ne.’ Sai a shafi na 37 an hade kalmar ‘kayi’ a maimakon ‘ka yi’ da ‘yayi’ a maimakon ‘ya yi.’ Kadan ke nan daga cikin kalmomin da aka yi kuskuren rubuta su.
Kodayake an yi kokarin takaita littafin ta yadda aka hada wasu abubuwa wuri guda amma da an fadada shi zai ba da damar a yi bayanin wadansu abubuwa dalla-dalla. Kamar a muhimmancin aikin Hajji da sharudda a kan wajabcin Hajji da Rukunan Hajji da Farillan Hajji, duk da an yi musu babi mai zaman kansa da ya fi gamsar da mai karatu a maimakon a takaita su.
Tsarin da aka yi na hada rubutun Hausa da na Larabci ya yi daidai, domin yin hakan zai ba maniyyaci damar gane yadda ake fadar misali niyyar Hajji ko Umra da Larabci kuma zai ba shi damar ya gane wasu abubuwa da yadda ake fadar su da Larabci kamar yadda shari’a ta tanada.
Wani abu da ya rage wa littafin armashi shi ne rashin sanya hotuna da ba a yi ba a littafin. Da an sanya hotuna da littafin ya kara kima da kwarjini da kuma jan hankalin mai karatu. Kodayake hotunan da aka sanya a bangon littafin na dakin Ka’aba da kuma wanda aka sanya a bangon baya na littafin duk sun dace. Don yin hakan zai sa littafin ya bayyana sakon da yake cikinsa tun kafin mai karatu ya karanta shi.
Shafukan littafin an shirya su bi-da-bi a cikin tsari amma yadda shafi na 25 ya zama babu komai a cikinsa na rubutu ya rage wa littafin armashi. Saboda haka nake shawartar Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano idan za ta sake duba littafin a sanya shafi na 25 don bayanin da ake cikinsa bai fito ba.