Littafin Jawabi A Kan Boko Haram a ma’aunin nazari

Sunan Littafi: Jawabi A Kan Boko Haram, Bisa Nazarin MusulunciMarubuci: Shaik Muhammad Sani Yahya JingirShafuka: 20. Shekarar Wallafa: 2011 Mawallafa: JIBWIS, Jos Rikicin da aka shiga na rashin tsaro saboda hare-haren da kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnati Lidda’awati Wal Jihad wacce ake kira Boko Haram take kai wa a sassa da dama na kasar nan shi […]

Littafin Jawabi A Kan Boko Haram a ma’aunin nazari
Littafin Jawabi A Kan Boko Haram a ma’aunin nazari

Sunan Littafi: Jawabi A Kan Boko Haram, Bisa Nazarin Musulunci
Marubuci: Shaik Muhammad Sani Yahya Jingir
Shafuka: 20. Shekarar Wallafa: 2011
Mawallafa: JIBWIS, Jos

Rikicin da aka shiga na rashin tsaro saboda hare-haren da kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnati Lidda’awati Wal Jihad wacce ake kira Boko Haram take kai wa a sassa da dama na kasar nan shi ya sa shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Izala, Shaik Yahya Jingir ya rubuta littafin nan da muke nazari a yau.
Babu shakka zubi da tsarin littafin ya dace da sunan da aka sanya masa, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ke cikinsa. Misali, yadda a shafin farko aka tsara abubuwa da ke cikin littafin, kamar gabatarwa da takaitaccen bayani a kan ’yan Boko Haram da ma’anar boko da hanyar yakar Musulmi da sauran kasashen duniya na tsarin Turawan mulkin mallaka da karantarwar Musulunci da tufka da warwara a tsarin Boko Haram da abubuwan lura da nasiha ga al’ummar Musulmi da jagororin al’umma da kuma rufewa.
Jigon littafin ya fito sosai idan aka yi la’akari da yadda malamin ya takaita bayaninsa a kan babin da yake magana a kansa, ba kamar wasu marubuta ba da za ka ga wani lokaci suna barin ainihin maudu’in da suke magana a kai. Misali, tun daga shafi na farko zuwa na karshe ya tsaya a kan manufar littafin.
Marubucin ya yi amfani da hikima wajen fadakar da jama’a kan illolin kungiyar Boko Haram da kuma yadda akidojinta suka saba wa koyarwar Musulunci, inda a shafi a 2 na littafin ya fara bayar da takaitaccen bayani a kan ’yan kungiyar.
Malamin ya yi kokari sosai saboda yadda ya binciko alakar ’yan Boko Haram da ’yan kala-kato, wadanda ba ruwan su da hadisan Manzon Allah sai dai son rai. Shi ya sa a shafi na biyar ya kawo misalai da yawa da za su gamsar da mai karatu.
Hakazalika, tsarin da ya yi amfani da shi na kawo ayar Alkur’ani a cikin harshen Larabci sannan ya fassara ta da harshen Hausa shi ma zai saukaka wa mai karatu zurfin binciken inda ayar take a cikin Alkur’ani ba tare da wata matsala ba. Misali, shafi 8 da na 9 da na 12 da na 15 da na 19 ya kawo ayoyi daban-daban da suke nuna muhimmacin neman ilimi da illar kashe rai ba da hujja ba amma a shafi na 10 ya kawo hadisin da yake nuna muhimmancin neman ilimi.
Kodayake littafin ya tsaru sosai amma akwai kura-kurai na dab’i da ka’idojin rubutu. Misali, a shafin farko na littafin an yi kuskuren hade kalmar ‘akan’ a maimakon ‘a kan.’ A shafi na 2 an hade kalmar ‘kungiyace’ a maimakon ‘kungiya ce’ da hada kalmar ‘za’a’ a maimakon ‘za a’ shafi na 4 da hada kalmar ‘haddaceshi’ a maimakon ‘haddace shi’ a shafi na 13.
Sannan ba a yi amfani da haruffan Hausa na ‘b’ da ‘d’ da ‘k’ ba. Misali a shafi na 20 an rubuta kalmar ‘wadannan’ a maimakon ‘wadannan.’ A shafi na 2 an rubuta kalmar ‘takaitacce’ a maimakon ‘takaitacce.’

Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah

Abba El-Mustapha ya samu lambar yabo kan yaƙi da cin hanci

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF