Littafin tambayoyi 100 na mata a ma’aunin nazari
Sunan littafi: Tambayoyi 100 Littafi: Kashi na farkoMawallafi: Shaik Muhammadu Ibni Salih UsaiminBugun farko: Saudi ArebiyaFassara: Ustaz Ahmad Adam KutubiBugun gida: Auwal Kutubi JosYawan shafuka: 40 kalubale da matsalolin da suka dabaibaye mata dangane da jinin haila da jinin biki cikin salla da azumi da aikin hajji shi ya sa fitaccen malamin nan na kasar […]
Sunan littafi: Tambayoyi 100
Littafi: Kashi na farko
Mawallafi: Shaik Muhammadu Ibni Salih Usaimin
Bugun farko: Saudi Arebiya
Fassara: Ustaz Ahmad Adam Kutubi
Bugun gida: Auwal Kutubi Jos
Yawan shafuka: 40
kalubale da matsalolin da suka dabaibaye mata dangane da jinin haila da jinin biki cikin salla da azumi da aikin hajji shi ya sa fitaccen malamin nan na kasar Saudi Arebiya Shaik Muhammadu Ibni Salih Usaimin ya rubuta littafi da harshen larabci ya lakaba masa suna ‘Tambayoyi 100’ kuma ya bayar da amsoshin su daki-daki, sannan Ustaza Ahmad Adam Kutubi ya fassara cikin harshen Hausa. Wannan shi ya sa mu ma muke nazarin littafin a wannan mako.
Babu shakka littafin ya amsa sunansa idan aka yi la’akari da ainihin a kan abin da aka yi magana a kai. Wanda ya rubuta littafin ya yi hikima da ya tsara shi bisa tsarin tambaya da amsa ta yadda zai yi saukin fahimta da ganewa ga duk wanda ya karanta shi ba tare da wata matsala ba.
Bugun da aka yi wa littafin cikin harshen Larabci da kuma harshen Hausa duk sun yi kyau saboda ba a yi kwauro ba. An sanya masa launi mai jan hankali tare da hoton ’yan mata suna koyon karatu a aji tare da malamarsu a gefe. Hakazalika hoton husumuyar masallaci da bishiyar dabino da ke jikin bangon littafin sun kara fito da littafin ta yadda zai ja hankalin mai karatu daga nesa.
Mai littafin bai bata lokaci ba wajen yin dogon bayanin gabatarwa ba ,haka shi ma mai fassara littafin bai bata lokaci wajen fasssara shi ba, domin ya tafi kai tsaye ya fassara abin da malamin ya rubuta. Ba kamar wasu masu fasssara ba inda za ka ga sun sanya ra’ayoyinsu yayin da suke fassara littafi. Wasu ma maimakon su yi fassarar da ta dace sai ka ga sun kare da sanya ra’ayinsu.
Jigon littafin ya fito sosai saboda irin yadda aka tsara shi bisa tambaya da amsa ta yadda da mutum ya karanta shi zai gamsu sosai. Duk da kokarin da mai fassara ya yi wajen fassara littafin tare da zabin kalmomin da suka dace littafin cike yake da kurakuren ka’idojin rubutu.
Kalmomin da ya kamata mai fassara ya hade sai ya raba su wadanda ya kamata ya raba sai ya hade su hakan ya janyo kalmomin ba sa karantuwa cikin sauki. Misali shafi na daya ya hade ‘ciwoba’ a maimakon ya raba su ‘ciwo ba’ , ya hade kalmar ‘batayi’ a maimakon ‘ba ta yi’ da kalmar ‘yakai’ a maimakon ‘ya kai’. A shafi na 14 ya hade kalmar ‘suyi’ a maimakon ‘su yi’ a shafi na 20 ya hade kalmar ‘dalibace’ a maimakon ‘daliba ce’ a shafi na 25 ya hade kalmar ‘tayi’a maimakon ‘ta yi’ a shafi na 31 ya hade kalmar ‘naji’ a maimakon ‘na ji’ da hade kalmar ‘tayi’ a maimakon ‘ta yi’.
Hakazalika, mai fasssarar ya rika mantawa da harufan da suke da lankwasa kamar ‘k’ da ‘b’ da ‘d’. Misali a shafi na 1 ya rubuta kalmar ‘baki’ a maimakon ‘baki’a shafi na 5 da na 7 da na 15 da na 20 da na 22 da na 39 da kuma shafi na 40 ya rika rubuta kalmar ‘radadi’ a maimakon ‘radadi’ da kalmar ‘habo’ a maimakon ‘habo’da kalmar ‘digo’ a maimakon ‘digo’ da kalmar ‘biki’ a maimakon ‘biki’.
Sai dai duk da haka littafin ya fito da abubuwa da yawa da suka shafi mata, ban da jinin haila da jinin biki da jinin Istahada, an amsa tambayoyi kan alwala da azumi da haduwar wankan janaba da na biki a lokaci guda da hukuncin mace mai al’ada da karatun Al’kur’ani da batun mata da biyan bashin azumi da hukunci kan shan maganin hana haila don yin azumi da hukuncin alwalar mace mai yoyon ruwa da hukuncin jinin biki da ke fitowa mata kafin haila da hukuncin haila kan mace mai aikin hajji da umara da hukuncin neman aure a kan neman auren wani da hukunci kan iyaye masu kashe auren ’ya’yansu da kuma wasu hukunce-hukunce kan saki da mayar da aure.
To ko me ne ne dalilin da ya sa littafin ya amsa tambayoyi dari da biyu a maimakon tambayoyi 100 kamar yadda aka yi masa take?. Wannan wanda ya rubuta littafin da wanda ya fassara ne kawai za su iya bada amsa.