Littafin Tarihin Ja’afar a ma’aunin nazari

Sunan littafi: Rayuwata Ta Ilimi Da Ta Da’awa – Shaikh Ja’afar Mahmud AdamMarubuci: Abdullahi Aliyu MusaShekarar Wallafa: 2013Yawan Shafuka: 64Kamfanin Wallafa: Ba a ambata ba Abubakar Haruna, a Legas Irin fice da sunan da marigayi Shaik Ja’afar Mahmud Adam ya yi a duniya da kuma irin gwagwarmayar da ya sha wajen yada addinin Musulunci da […]

Littafin Tarihin Ja’afar a ma’aunin nazari
Littafin Tarihin Ja’afar a ma’aunin nazari

Sunan littafi: Rayuwata Ta Ilimi Da Ta Da’awa – Shaikh Ja’afar Mahmud Adam
Marubuci: Abdullahi Aliyu Musa
Shekarar Wallafa: 2013
Yawan Shafuka: 64
Kamfanin Wallafa: Ba a ambata ba

Abubakar Haruna, a Legas

Irin fice da sunan da marigayi Shaik Ja’afar Mahmud Adam ya yi a duniya da kuma irin gwagwarmayar da ya sha wajen yada addinin Musulunci da kuma dimbin masu sauraron karatunsa, su ne suka sanya a yau muke nazarin littafin tarihin rayuwarsa; Shaik Ja’afar Mahmud Adam, wanda Malam Abdullahi Aliyu Musa ya rubuta, wanda ya yi masa lakabin: ‘Rayuwata Ta Ilimi Da Ta Da’awa – Shaik Ja’afar Mahmud Adam.
Babu shakka littafin ya amsa sunansa, idan aka yi la’akari da yadda aka tsara shi daki-daki, inda aka fara bayyana abubuwan da littafin ya kunsa kamar gabatarwa da sharhin Dokta Muhammad Sani Umar da sharhin Shaikh Abdulwahab Abdalla da sharhin Dokta Abdullahi Fakistan da godiya da gabatarwar marubuci da sadaukarwa da rayuwata ta ilimi da ta da’awa a Kano da rayuwata ta da’awa a Borno da kuma kammalawa.
Marubucin ya yi kokari kwarai da gaske saboda kiyaye ka’idojin rubutu da ya yi ta hanyar yin rubutu ba tare da kwamacala ba. Duk kalmar da ya kamata ta zama a rabe ya rabe, wacce ya kamata ta zama a hade ya hade sai dai ’yan kurakuren da ba a rasa ba. Wani abun sha’awa shi ne yadda marubucin ya rubuta kalmomi masu rikitarwa cikin tsari tare da bin ka’idar rubutu. Misali, a shafi na 4, a sakin layi na karshe ya rubuta kalmar Jita-jita da shaci-fadi daidai cikin tsari. Haka ma haruffan ‘k’ da ‘b’ da ‘d’ ya yi kokarin rubuta su ta hanyar da ta dace ba kamar sauran marubuta ba da suke rubuta littattafansu babu ka’idar rubutun Hausa.
Duk da haka marubucin ya yi tuntuben alkalami a wurare kalilan. Misali, a shafi na 5 ya rubuta kalmar ‘kunsa’ a maimakon ‘kunsa’ sannan a wasu lokuta ya rika yin amfani da sakkwatanci a maimakon daidaitacciyar Hausa. Misali, a shafi na 45 ya rubuta ‘Ubangiji Ta’ala shi yafe mana’ a maimakon ‘Ubangiji Ta’ala ya yafe mana.’
To sai dai duk da haka littafin ya kawo maganganun Malam Ja’afar masu jan hankali da ban tausayi da jaruntaka da jajircewa da tawali’u da kuma karfafa gwiwa. Misali, a shafi 30 har zuwa na 40, inda Malam Ja’afar yake bayyana malaman da ya yi karatu a wurinsu, tun daga garin Daura da Kano har zuwa Jami’ar Madinah. Sannan kuma ya bayyana sunayen abokan karatunsa da kuma wadanda suka taimaka masa wajen yada addini da kuma neman iliminsa tare da wadanda suka taimaka masa a rayuwa ta yau da kullum. Daga bisani a shafi na 44 sai ya ce: “Ya ’yan uwa, hakikanin gaskiya wannan gamon-katar ne na Ubangiji ba dabarar dan Adam ba ce.”
Wata magana da marubucin ya kawo a shafi na 61 zuwa na shafi 62 na littafin, wadda ita ce maganar da Malam Ja’afar ya yi a karshen rayuwarsa ita ce lokacin da ya nemi mutane su yafe masa, shi ma kuma ya yafe wa kowa da kowa inda ya ce: “Sannan kamar yadda na fada, daga karshe nake rokon ’yan uwa, dukkan wanda na yi masa ba daidai ba, don Allah ya yafe mini, sawa’un cikin maza ko cikin mata. dan Adam zai iya yi wa mutum laifi wanda yake cikin sani ko wanda ba ya cikin sani kuma ina son mu yi amfani da wannan dama mu roki Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala Ya yafe mana kura-kuranmu.”

Abba El-Mustapha ya samu lambar yabo kan yaƙi da cin hanci

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana