Littattafan Tom Clancy sun kara kwarjini bayan mutuwarsa
Thomas Leo, wanda aka fi sani da sunan Tom Clansy Jr. kwararre kuma shahararren marubucin littattafan kirkirarrun labarun yaki ne, dan kasar Amurka. A makon jiya ne, 1 ga Oktoba ya mutu a asibitin Johns Hopkins da ke Baltimore, a kasar Amurka. Ya mutu yana dan shekara 66 a duniya.An haife shi ne a ranar […]
Thomas Leo, wanda aka fi sani da sunan Tom Clansy Jr. kwararre kuma shahararren marubucin littattafan kirkirarrun labarun yaki ne, dan kasar Amurka. A makon jiya ne, 1 ga Oktoba ya mutu a asibitin Johns Hopkins da ke Baltimore, a kasar Amurka. Ya mutu yana dan shekara 66 a duniya.
An haife shi ne a ranar 12 ga Afrilu, 1946 a garin Baltimore da ke Jihar Maryland, kasar Amurka.
Tom Clancy. Marubuci ne da ya kware wajen rubuta littattafan kirkirarrun labarun zamani da suka shafi yake-yake da sauransu. An dade ana mayar da littattafansa zuwa fim, wadanda suka hada da ‘The Hunt for Red October’ da sauransu.
kwararren marubucin, ya yi karatunsa ne a Jami’ar Loyola da ke Maryland, daga 1965 zuwa 1969.
Wani abin al’ajabi shi ne, duk da cewa littattafansa suna tashe, amma rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan mutuwarsa, sai makaranata suka kara himmatuwa wajen rububin littattafan nasa. Littattafansa biyar da suka samu babbar kasuwa daga mutuwarsa sun hada da: ‘Threat becto’ da ‘Without Remorse’ da ‘Dead or Alibe’ da ‘Locked On’ da kuma ‘Against All Enemies.’