Liverpool ta kulla yarjejeniyar shekara 5 da Mac Allister

Na zaku na soma murza leda a kungiyar.

Liverpool ta kulla yarjejeniyar shekara 5 da Mac Allister

Liverpool ta kammala sayen dan kwallon Argentina, Alexis Mac Allister a kan kudi fam miliyan 35 daga Brighton.

Dan kwallon ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara biyar.

Ya taimaka wa Brighton wajen samun gurbi a Gasar Europa da za a buga a kakar wasa mai zuwa.

Dan shekara 24, Mac Allister ya zura kwallo 20 a wasa 112 da ya buga wa Brighton, sannan ya taimaka wa Argentina lashe Kofin Duniya a bara.

“Mafarkina ya zama gaskiya, na zaku na fara murza leda,” in ji Mac Allister.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na kokarin kara karfin tawagarsa sakamakon ficewar ’yan wasan tsakiya irinsu James Milner, Naby Keita da Alex Oxlade-Chamberlain.

Mac Allister ya koma Brighton ne daga kungiyar Argentinos Juniors a watan Janairun 2019.

Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine

Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi

Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala

Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya