Liverpool ta lallasa Manchester United har gida

Manchester United na mataki na 13 a teburin gasar.

Liverpool ta lallasa Manchester United har gida

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta doke abokiyar hamayyarta, Manchester United har gida da ci uku da nema.

Wannan na zuwa ne bayan karawa da ƙungiyoyin biyu suka a gasar Firimiyar Ingila ta bana, a mako na uku.

Manchester United ta yi rashin nasara a wasanni biyu daga cikin uku da ta buga bayan fara gasar Firimiyar ta bana.

A makon da ya gabata ƙungiyar ta yi rashin nasara da ci 2 da 1 a hannun Brithtom Hove & Albion.

Manchester United ta samu nasara ne a wasa ɗaya kaɗai, inda ta doke Fulham a wasan farko na gasar.

’Yan wasan gaban Liverpool, Luis Diaz da Mohamed Salah ne suka jefa wa ƙungiyar ƙwallon uku.

Yanzu haka Liverpool na mataki na biyu da maki tara a teburin gasar, yayin da Manchester United ke mataki ma 13 da maki 3.