Liverpool ta sayar da wani bangare na hannun jarinta

Mamallakan Liverpool na son ci gaba da rike mafi rinjayen hannayen jarin.

Liverpool ta sayar da wani bangare na hannun jarinta

Kamfanin FSG da ke da mallakin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya amince da sayar da wani bangare na hannayen jarin kungiyar.

Bayanai sun ce darajar hannun jarin da aka sayar ta kai fam miliyan 82 da fam miliyan 164 ga katafaren kamfanin zuba jari a bangaren wasanni na kasa da kasa da ake kira Dynasty Equity.

Tun farko FSG da kansa ya yi shelar neman masu sayen wani bangare na hannayen jarin kungiyar a kokarin warware basukan bankin da suka yi ma ta katutu.

An sanya hannun jarin a kasuwa duk da cewa mamallakan na Liverpool na son ci gaba da rike mafi rinjayen hannayen jarin don samun karfin fada aji a kungiyar.

Shugaban kamfanin na FSG, Mike Gordon ya ce kamar ko yaushe kamfanin na da karfin fada a ji a Liverpool duk da yadda ya sayar da wani bangare na hannayen jarin.

Liverpool dai ta yi asarar fam miliyan 100 na kudaden shiga a lokacin annobar Covid-19 yayin da kuma kulob din ya kashe fam miliyan 50 wajen ginin sabon sansanin atisayensa na Kirkby da aka bude a 2020.

Kazalika, Liverpool ta kashe wasu fam miliyan 12 na daban da kungiyar ta sanya wajen sayen tsohon sansanin atisayenta na Melwood da ta bai wa tawagar mata.

Baya ga wannan, kungiyar ta kashe kudin da yawansa ya kai fam miliyan 145 wajen sayen ‘yan wasa irinsu Dominik Szoboszlai da Alexis Mac Allister da kuma Wataru Endo baya ga Ryan Gravenberch a kasuwar musayar ’yan wasan da ta gabata.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja