Lokaci: A cikinsa ake shuka alheri ko sharrin da za a girba Ranar Lahira
Masallacin Khidmatul Wadaniyya, Khartoum Sudan Hamdala da taslim: Bayan haka, babu wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar Musulmi. Idan Musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne Sallar Asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar, haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta […]
Masallacin Khidmatul Wadaniyya, Khartoum Sudan
Hamdala da taslim:
Bayan haka, babu wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar Musulmi. Idan Musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne Sallar Asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar, haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta don ya gana da Ubangijinsa. A mako kuma akwai Sallar Juma’a, a shekara akwai watan azumi, akwai Sallar Idi, akwai Idin Layya, akwai aikin Hajji. Idan Musulmi yana da dukiya kuma akwai fitar da zakka duk shekara.
Allah Ya rantse da lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci ga dan Adam shi ne jarinsa, kai shi ne rayuwarsa, a cikinsa ne kake murna ko ka samu damuwa, a cikinsa kake ciwo ko ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake shuka alheri ka girbe shi a Lahira ko ka shuka sharri ka same shi yana jiran ka gobe kiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne ake samun Aljanna ko a fada cikin Jahannama, Allah Ya kiyaye mu.
Lokaci ya fi komai saurin wucewa, ba ya jira, kuma in ya tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai sanar da kowa lokacin da Ya diba masa ba. Lokacin da Allah Ya ba ka shi ne tsawon shekarun rayuwarka, idan ka kwantar da hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da bai da yawa. Wanda aka ba shi shekara 60 misali nawa ne za a cire daga cikin kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci? Nawa ne adadin kwanaki marasa amfani a cikinsu?
dan Adam yakan yi nadama a kan lokacinsa da ya wuce a wurare muhimmai guda biyu: Na farko: Idan Mala’ikan mutuwa ya damke shi, ya hakikance cewa tilas zai bar duniya a nan yake cewa: “Ya ubangiji Ka dawo da ni, domin kila in yi aikin kwarai a cikin abin da na bari. Ina! Wata magana dai ce da shi yake fadar ta, kuma a bayansu akwai rayuwar barzahu da za su yi har zuwa ranar da za a tashe su. (Muminun: 99-100). Wuri na biyu: Shi ne idan aka yi tashin Alkiyama, kowa ya ga sakamakonsa, aka yanke wa kowa hukuncin in da zai zauna. A nan ne dan Adam ke cewa: “Kuma da za ka ga kangararru sun sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, (suna cewa): “Ya ubangijinmu! Mun fa gani kuma mun jiya, to, Ka mayar da mu mu yi aikin kwarai, mu fa tabbas mun gano gaskiya.” Kuma da Mun so da Mun bai wa kowane mai rai ikon shiriya, amma maganarMu ta riga ta tabbata cewa, lallai sai Mun cika wutar Jahannama da aljanu da mutane baki daya. To, ku dandani azaba don mantawar da kuka yi da haduwarku da wannan rana, Mu ma Mun manta da ku, kuma ku dandani azaba ta dindindin saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.” (Sajdah: 12-14).
Manzon Allah (SAW) ya ce, “Akwai ni’imomi guda biyu da ake kwarar dan Adam a kansu; lafiya da lokaci.” Dalilai uku ne ke sa a kwari mutum game da lokaci. Kodai ya kasance bai yi cikakken amfani da lokacin ba ta hanyar yin abin da ya kamata wanda zai samu babban lada, ko ya kasa yin aikin ladan sam sam, ko kuma a cikin lokacin ya yi aikin zunubi. Mutane sun kasu kashi-kashi dangane da lokaci. Wani za ka ga mafi yawan lokacinsa yana cike da abubuwa masu amfani, wani duk lokacinsa na sharholiya ne, wani kuma bai ma san ya zai yi da lokacin ba! Matsalar wani ita ce bai tsara wa rayuwarsa komai ba, wani bai san muhimmancin lokacin ba. Wani ya sani amma bai da karfin zuciya da kwarin gwiwar maida hankali ga abin da ke amfaninsa.
Yana da kyau mu duba rayuwar magabata mu ga yadda suke cin moriyar lokaci. Abdurrahman bin Mahdi ya ba da labarin malaminsa Hammad bin Salamah ya ce, da an ce wa Hammad ga Alkiyama nan za ta tsayu bai da yadda zai kara bisa ga aikin da yake yi. Ba za mu yi mamakin wannan maganar ba in muka san cewa Malam Hammad ya rasu yana cikin Sallah. Saurari abin da wani dalibin ilimi Abu Hatim Ar-Razi (Rahimahullah) yake cewa: “Mun nemi Malam Ka’anabi ya karantar da mu Muwadda sai ya ce, to ku zo da safe. Sai muka ce masa da mun yi Asuba wurin Malam Hajjaj muke zuwa. Ya ce, to ku zo in kun kare. Muka ce sannan muke zuwa wurin Malam Muslim bin Ibrahim. Ya ce to ku zo in kun gama. Muka ce ko da muke gamawa Azahar ta yi, sannan muke karatu ga Abu Huzaifa. Ya ce, to, ku zo bayan La’asar. Muka ce, makarantar Arim. Ya ce to ku zo bayan Magariba. To, daga nan muka rika zuwa wurinsa idan an yi Magariba sai ya fito ana sanyi ya nade kansa ya yi ta karantar da mu har illa masha Allahu.”
Ta hanyar amfani da lokaci ne kawai ake iya fito da baiwa iri-iri da Allah Ya yi wa dan Adam. Bincike ya nuna cewa akasarin mutane ba su amfani da kashi 25 cikin 100 na baiwar da Allah Ya ba su. Yaron da ya fadi jarrabawa kuma ya rufe aji yana iya zama na daya ba a makarantarsu kawai ba a fadin jiha inda aka yi kokarin fitowa da baiwar da Allah Ya ba shi. Shiriritaccen da za ka gan shi yana kashe wando a bakin titi yana iya zama babban malami ko babban mawallafi ko kwararren likita ko gogaggen dan siyasa ko fitaccen dan kasuwa. Amma an watsar da baiwar da Allah Ya ba shi, shi ya sa ya lalace. Wanda ya zo na baya a wajen tsere ko gasar karatun Alkur’ani yana iya zarce kowa in da an tona baiwar Allah da ke tattare a cikinsa. Kana iya gwada wannan ga dan takara a wajen tseren gudu idan ya kasa, ya koma baya har ya kai ga faduwa saboda gajiya. Idan likitoci suka auna shi a lokacin za su ce mana akwai sauran karfi da kuzari mai yawa a jikinsa amma yana bukatar abin da zai zakulo wannan karfin. Yaya za mu gane wannan? Mu sakar masa zaki ko maciji misali. A nan ne za ka sha mamaki. Suna yin arba da zaki za ka ga ya tashi ya ruga da gudu, irin gudun da can da farko ma bai yi shi ba. Me ya tono wannan kuzari na gudu daga jikinsa? Daga sama aka sauko masa da shi? A’a. Dama yana nan cikin jikinsa amma yana neman abin da zai motsa shi! Wannan shi zai fassara maka irin albarkar rayuwar magabata wajen jihadi da karantarwa da rubuce-rubuce da makamantansu. Sun sanya wata manufa a gabansu ita ce neman yardar Allah. Wannan manufa sai take fitar da iyakar abin da yake yiwuwa na baiwa da ke cikinsu. In ba don Manzon Allah (SAW) ba, da su Sayyidina Umar da Ibnu Mas’ud da Khalid bin Walid da sauransu duk iyakarsu su zamo makiyaya ko ’yan kasuwa ko ’yan tauri ko wani abu mai kama da wannan. Amma da aka samu jagora cikakke mai manufa sai ya fito da ikon Allah a cikinsu. Nan take kowanensu ya taka rawa mai muhimmanci a tarihin duniya. Wani daga cikin magabata ya ce, wani lokaci sai barci ya fara dauka ta, ina cikin jin dadinsa sai in tuna da wuta da Aljanna. Idan na tuna haka sai in ga na zabura kamar zaki na tafi zuwa kiyamullaili.