Lokaci: A cikinsa ake shuka alheri ko sharrin da za a girba Ranar Lahira (2)

Masallacin Khidmatul Wadaniyya Khartoum Ko kun ga yadda tsayayyar manufa take sa a kula da muhimmancin lokaci? Fetur idan aka zubar da shi ga kasa sai kasa ta shanye shi bai amfani kowa ba. Amma in da an zuba shi a mota fa? Wannan shi ne misalin hikimomin Allah da ba mu yi amfani da […]

Lokaci: A cikinsa ake shuka alheri ko sharrin da za a girba Ranar Lahira (2)

Zaune Dokta Mansur Sakkwato kafin gabatar da Huxubar. Hoto daga Dandalin Sanin Martabar Sahabbai.

Masallacin Khidmatul Wadaniyya Khartoum Ko kun ga yadda tsayayyar manufa take sa a kula da muhimmancin lokaci? Fetur idan aka zubar da shi ga kasa sai kasa ta shanye shi bai amfani kowa ba. Amma in da an zuba shi a mota fa? Wannan shi ne misalin hikimomin Allah da ba mu yi amfani da lokaci muka ci moriyarsu ba. Wannan kuma shi ne sirrin da ya sa idan an yi yaki Musulmi ke galaba a kan kafirai. Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma kada ku yi rauni wajen yakar mutanen, in har kuna jin radadi, to hakika su ma suna jin radadi kamar yadda kuke ji, kuma kuna fatar samun abin da ba su fatar samunsa daga wurin Allah. Kuma Allah Ya kasance Mai cikakken sani, Mai cikakkiyar hikima.”  (Nisa’i: 104).  A wata ayar kuma Allah Ya ce: “Kuma kada ku yi rauni, kada ku yi bakin ciki, domin ku ne madaukaka in kun kasance muminai.” (Ali-Imran:139).

Wani malami ya tsaya a gaban ’yan wasa suna ta sharholiyarsu. Sai aka ga yana jin haushi yana ciza yatsa. Don me? Ya ce, wallahi na so a ce lokaci kaya ne, da sai in saye na wadannan don na ga ba ya da amfani a gare su.

Ya ku bayin Allah! Ga wasu muhimman shawarwari da za su taimaka mana wajen kula da lokaci:

  1. Kada ka yarda ka bar wani lokaci fanko, domin wannan ba dabi’ar mumini ba ce. Allah Ta’ala Ya ce: “Idan ka gama al’amurran duniya, to ka kafu wajen ibada. Kuma ka yi kwadayi zuwa ga Ubangijinka.” (Sharh: 7 -8). Da zarar ka samu lokacin da ba abin da za ka yi, samar masa wani abin da zai amfane ka. Misali lokacin jiran wani, kamar jiran likita a asibiti, ko layin shiga mota, ko kuma kan hanya daga wani gari zuwa wani gari ko wata unguwa zuwa wata. A lokacin da kake tuka babur ko aka dauke ka a kansa zuwa kasuwa. A lokacin da kake shago amma ba wani abokin ciniki tare da kai. A duk irin wadannan lokuta kana iya kago wani abu da zai amfane ka kamar yin zikiri ko karanta wani littafi ko wata tattaunawa mai muhimmanci da wani wanda kake tare da shi. Da wannan ma’aikaci na iya cin moriyar abin da ya yi rara na lokacinsa. Dan kasuwa ma haka, mai acaba da mai lodi da kafinta da mai kasa kaya a titi, duk suna iya amfani da rarar lokutansu wajen ambaton Allah da makamantansa. Abdussalam yakan ce wa dansa Ibnu Taimiyya, Ahmad: “Zo ka yi karatu kusa da ban-daki kafin na fito,” don ya saurari karatu a yayin da yake biyan bukata, gudun kada lokacinsa ya tafi a banza a daidai wannan lokaci.
  2. Yi kokari a kullum ka gabatar da abin da ya fi muhimmanci. Idan ayyuka biyu suka hadu babba da karami ka fara gabatar da babba. Idan kuma dayansu yana amfaninka ne kai kadai dayan kuma yana amfanar jama’a, fara mai amfanar jama’a tukuna. Kamar Sallar Nafila da karantar da mutane. Idan kuma aiki daya yana da lokaci mai wucewa dayan kuma ana iya yin sa a koyaushe, to, fara gabatar da wanda lokacinsa ke wucewa, kamar addu’a a lokacin ijaba.
  3. Ka auna duk maganar da za ka yi don ka tantance amfaninta ko cutarwarta. Idan ka yarda ba ta da amfani sai ka bar ta, ka yi wata ko ka yi shiru don ka tsira da lokacinka.
  4. Yi kokari ka gano lokutan da kake tozartawa a wuni. Misali, daga Sallar Asuba zuwa karfe goma, awa ne? Wane amfani suke maka? Kada ka manta cewa, kafin wannan lokaci ka share dare watakila kana barci. Tsakanin Magriba da Isha’i me kake yi? Daga Isha’i zuwa shiga barci fa? Idan ka gano wadannan lokutan sai ka tsara yadda za ka rage tozarta su.
  5. Kada ka bari mutane su rika juya lokacinka. Dubi misali yadda Imam Bukhari yake yi idan ya yi bako mai nauyi. Abin da yake yi shi ne sai ya dauko littafinsa ya ce wa bakon yana da kyau mu karanta wannan domin mu amfana. Shi kuma Ibnu Akil Al-Hambali idan ya yi irin wadannan baki sai ya dauko alkalumansa na rubutu ya ce su taya shi fekewa.
  6. Tuna mutuwa na taimaka maka ainun wajen kula da lokacinka. Duk matafiyi idan ya ci rabin hanya zai ji cewa ya kusa kaiwa. Amma a mas’alar rayuwa da mutuwa ba mu tuna haka. Sai ka ga mutum in ya yi shekara talatin yana ganin tukuna bai yi komai ba. Shi ya sa ake cewa mafi yawan mutane suna mutuwa ne a cikin kuruciya, don ba a dauka sun kai lokacin mutuwa ba. Rayuwar dan Adam ba ta da tsawo. Akwai halittu na daji da ke kai shekara 200 zuwa 300 ko abin da ya fi haka. A bishiyoyi ma akwai wadanda kunne ya girmi kaka. Su duwatsu ba a ma maganarsu. Don haka babu mamaki ka ga shekarunka sun kare nan take. Samu wata rana koda a cikin wata ne ka je ziyara makabarta kai kadai ka tsaya ka kalli wadanda ke kwance. Ka tambaye su, mene ne gurinku? Me kuke fata a yau? Ba za su ba ka amsa ba. Amma ka sani da za su buda baki da za su ce, muna son mu dawo duniya mu ci ribar lokaci.
  7. Sanin cewa bayan mutuwa akwai tambaya. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba wanda zai daga kafarsa a Ranar Alkiyama har sai ya amsa tambayoyi guda hudu:

Ta farko: Rayuwarsa a ina ya karar da ita?

Ta biyu: Kuruciyarsa a kan me ya tafi da ita?

Ta uku: Abin da ya sani ko ya yi aiki da shi?

Ta hudu: Dukiyar da ya samu a duniya, ta ina ya same ta kuma ta yaya ya kashe ta?

Ya ku ’yan uwa Musulmi! Mu ji tsoron Allah mu kyautata lokacinmu, mu amfana da shi.

Ya ku ’yan uwa Musulmi! Mu nisanci abubuwan da ke shafe albarka wadanda suka hada da saba wa Allah a cikin kowane irin sha’ani. A cikin ciniki misali rantsuwar karya da yaudara na shafe albarka. A sha’anin hulda ta kudi cin riba ko bayar da ita na shafe albarka. Haka ma rowa ga wanda Allah Ya wadata tana shafe albarkar kudin da mai kudin baki daya. Neman abinci ta hanyar roko ko bara ko damfara ko sata duk suna shafe albarka. Mu nisance su. Babu dukiyar da ke albarka ta zamo mai cikakken amfani in ba wadda aka nema ta hanya shari’antacciya ba. Idan kuma an samu a gode wa Allah; kada a yawaita dogon buri domin shi ma yana shafe albarka.

Ya Allah! Muna rokon Ka da sunayenKa kyawawa da siffofinKa madaukaka, Ka sanya albarka ga rayuwarmu da ayyukanmu da iyayenmu da iyalanmu da zuri’yarmu. Ya Allah Ka ba mu dukiya mai albarka, Ka zaunar da mu lafiya a cikin kasarmu, Ka shugabantar da mutanen kirki a kanmu. Ka dauke mana jarrabawar shugabanni barayi, azzalumai, mayaudara.

Ya Allah! Ka azurta mutanen Sudan (da sauran kasashen Musulmi) da rayuwa mai Albarka, Ka kare su daga fari da tashin hankali da annoba da musibu manya da kanana.

Allah Ka tsarkake zukatanmu da duk abin da muke aikatawa. Ka yi mana karshe mai kyau, mu gama lafiya, mu cika da imani.