Lokaci na neman kure wa Shugaban Kasa da gwamnoni –Yahaya Kega

Alhaji Yahaya Muhammad Kega jigo ne a Jam’iyyar APC a Jihar Filato kuma shi ne Shugaban Kungiyar Dillalan Mota ta Najeriya reshen jihar. A tattaunawa da wakilinmu kan yadda shugabannin kasar nan suke tafiyar da harkokin mulki, ya bayyana cewa lokaci na neman kure wa Shugaban Kasa da gwamnoni:   Yaya ka ga tafiyar Shugaban […]

Lokaci na neman kure wa Shugaban Kasa da gwamnoni –Yahaya Kega

Alhaji Yahaya Muhammad Kega jigo ne a Jam’iyyar APC a Jihar Filato kuma shi ne Shugaban Kungiyar Dillalan Mota ta Najeriya reshen jihar. A tattaunawa da wakilinmu kan yadda shugabannin kasar nan suke tafiyar da harkokin mulki, ya bayyana cewa lokaci na neman kure wa Shugaban Kasa da gwamnoni:

 

Yaya ka ga tafiyar Shugaban Kasa da gwamnonin jihohi, musamman ganin sun cika kwana 100?

Gaskiya za mu iya cewa al’ummar Najeriya ba abin da muka zata ba ke nan ga wadannan shugabanni. Domin alkawura suka yi mana muka zabe su, kuma alkawuran suna nan a kasa, kuma abin tambaya ne gare su.

Babu shakka tashin farko, ba mu gane ba, domin duk da cewa shugabannin sun cika kwana 100, da rantsuwa, yawaicinsu ba su yi nade-naden da suka kamata ba, domin tafiyar da gwamnatin. Ya kamata zuwa yanzu a ce kowa ya kammala shirya tafiyar gwamnatinsa, amma har yanzu wadansu ba su yi haka ba. Har yanzu wadansu gwamnoni, ba su nada kwamishinoni da mataimaka na musamman da za su rika shiga cikin jama’a suna jin koke-kokensu ba.

Wannan abin da ke faruwa ya nuna cewa akwai koma-baya. Ya kamata a ce kafin su cika kwana 100 da rantsuwa sun shirya tafiyar gwamnatocinsu ganin yawaicinsu suna wa’adi na biyu ne.

Duk inda aka yi shekara uku, shekara daya za ta zama lokacin yakin neman zabe na gaba ne.  Ya kamata mu gani a kasa a cikin kwana 100 da suka yi kan kujerun mulki. Amma gaskiyar magana  zuwa yanzu ba mu ga komai ba. A da mun dauka yawaicinsu aiki kawai za su sanya a gaba kan alkawuran da suka yi wa mutane kamar hanyoyin mota da inganta wutar lantarki da farfodo da masana’antu da samar da ayyukan yi da sauransu.

Yanzu al’ummar Najeriya suna cikin damuwa, ga miliyoyin matasa nan babu aiki a kasa. Ya kamata a ce zuwa yanzu shugabannin sun kirkiro wasu hanyoyi da za su samar wa matasan kasar nan ayyukan yi. Amma muna nan jiya i yau, gaskiya wadannan abubuwa suna damun mutane. Saboda haka ya kamata a samu canji na hakika, don lokaci yana kure musu. Kada Shugaban Kasa da gwamnonin jihohi su bari lokaci ya kure musu.

A ganinka wadanne muhimman abubuwa ne ya kamata Shugaban Kasa da gwamnoni su fi mayar da hankali a kansu?

Abin da ya kamata a mayar da hankali musamman a Gwamnatin Tarayya, shi ne tsaro, domin ya tabarbare. Maganar sace-sacen jama’a don neman kudin fansa ta yi yawa a kasar nan. Kuma har yanzu zaman lafiya yana danye ne domin abin da gwamnatin ta yi a baya, kan tsaro ya fi abin da take yi yanzu. Yanzu kamar abubuwa suna dawowa suna kara rikicewa. Kuma yawaicin abubuwan da suke faruwa kan tsaro ana danganta su ne da rashin ayyukan yi. Don haka ya kamata gwamnati ta bude hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan. Idan mutane suna da ayyukan yi, komai zai iya lafawa. Don haka Gwamnatin Tarayya ta fara bude masana’antu ta kyautata wutar lantarki ta samar hanyoyi da ruwan sha. Su kuma gwamnonin jihohi ya kamata, ’yan kudin da suke samu daga tarayya su rika amfani da su wajen ayyukan raya kasa da sauran ayyukan da za su samar da ayyukan yi ga al’umma. Ba wai da sun samu kudin su rika kashe su inda bai kamata ba. Domin matukar mutane ba su samu aikin yi ba, suna cikin wahala suna ci da kyar, kuma kasuwa babu dadi, ina tabbatar maka babu abin da za a iya gani. Don haka ya kamata gwamnoni su maida hankali kan wadannan abubuwa.

Shugabannin nan su sani mutane suna ta koke-koke a kasar nan, idan kasuwa mutum yake yi, ko aikin gwamnati ko ma me, babu wanda ba ya kokawa yanzu a Najeriya. Don haka gwamnati ta sake duba tsare-tsarenta, idan aka gwada wani tsari aka ga ba a samu nasara ba, sai a sake gwada wani tsarin.

Ganin abubuwan da suke faruwa, kana ganin jam’iyyarku ta APC za ta yi tasiri a zabubbukan shekarar 2023?

Idan har gwamnatocin da Jam’iyyar APC ta kafa suka yi abubuwan da suka kamata, jam’iyyar za ta iya samun nasara a zabubbukan shekarar 2023.      Kuma idan ka dubi wani bangare ba wadanda suke kan mulki ne za su sake tsayawa takara a zabubbukan shekarar 2023 ba, domin yawaicinsu suna wa’adinsu na karshe ne, musamman gwamnoni da Shugaban Kasa. Wadansu ’yan majalisa an riga an gaji da su, don haka za a iya canja su. Ina ganin idan ba wani abu ba, wannan jam’iyya ta APC za ta iya sake kafa gwamnati a Najeriya. Domin jam’iyyar kamar jam’iyya ce ta talakawa. Har yanzu  jam’iyyar ita ta fi kusa da talakawa, fiye da Jam’iyyar PDP. Har yanzu Jam’iyyar APC tana kusa da talakawa, kuma talakawa suna goyon bayanta. Domin gwamnatin APC, talakawa ne suka zabe ta, kuma   jam’iyyar ta wayar wa  talakan Najeriya kai ya gane ’yancinsa, ya gane cewa kuri’arsa ita ce ’yancinsa. Idan ka lura da zaben da ya gabata, wane irin kudi ne Jam’iyyar PDP ba ta fitar ba, don ta ci zabe, amma talakawa suka ki zabenta, suka zabi Jam’iyyar APC.