Lokaci ya yi da jihohi za su sama wa kansu wutar lantarki —Kwankwaso
Kwankwaso ya jaddada muhimmancin jihohi su fara samar wa kansu wutar lantarki
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana muhimmancin jihohi su fara samar wa kansu wutar lantarki.
Kwankwaso ya jaddada bukatar gwamnatocin jihohi su riƙa sama wa kansu lantarki ne a tsokacinsa kan lalacewar wutar da ta jefa yankin Arewa cikin duhu tsawon kwanaki takwas.
Ya ce, “abin takaici ne yadda akasarin yankin Arewa ke cikin duhu sakamakon lalata layin wutar lantarki mai ƙarfin 330kV da ke ɗauko wutar daga Shiroro zuwa Kaduna da ke kai wutar zuwa Kano da Kaduna da kuma ɗaya layin da ke kai wutar zuwa jihohin Bauchi da Gombe da sauran yankin Arewa maso Tsaki.
“Wannan matsalar ta ta’azzara tsadar man fetur tare da jefa iyalai da masana’antu cikin duhu.
- Manchester United ta sallami kocinta, Erik ten Hag
- Lokaci ya yi da jihohi za su sama wa kansu wutar lantarki —Kwankwaso
“Tsawon lokacin da aka ɗauka ba tare da gyara wutar ba ya nuna irin gazawar ɓangarenmu na wutar lantarki wanda ke buƙatar a magance domin daƙile aukuwar haka a nan gaba.
“Ya kamata mu duba wasu hanyoyin samar da lantarki da makamashi a Nijeriya daga albarkatun da Allah Ya huwace wa ƙasar.”
Don haka Kwankwaso ya bukaci gwamnatocin jihohi da ’yan kasuwa su zuba jari a bangaren samar da lantarki na zamani.
“Ina kira ga jihohi da ’yan kasuwa su duba wasu hanyoyin samar da wutar kamar yadda muka yi Jihar Kano inda muke amfani da iska a Challawa da Tiga, domin guje wa dogaro kan hanyoyin samar da wutar lantarki marasa nagarta.”