Lokaci ya yi da ’yan majalisa za su tsige Shugaba Jonathan

Anya kuwa ’yan Majalisar Dattawan Najeriya kun san me kuke yi a majalisa? Domin a gaskiya amincewar da kuka yi nan take na a ci gaba da kakaba dokar ta-baci ga jihohin Adamawa da Borno da Yobe ya nuna wa duniya cewa ku ’yan amshin shatan Shugaba Jonathan ne kawai. Domun kamata ya yi ku […]

Lokaci ya yi da ’yan majalisa za su tsige Shugaba Jonathan

Anya kuwa ’yan Majalisar Dattawan Najeriya kun san me kuke yi a majalisa? Domin a gaskiya amincewar da kuka yi nan take na a ci gaba da kakaba dokar ta-baci ga jihohin Adamawa da Borno da Yobe ya nuna wa duniya cewa ku ’yan amshin shatan Shugaba Jonathan ne kawai.

Domun kamata ya yi ku dauki matakin tsige Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ne yanzu tunda gwamnatinsa ta kasa samar da zaman lafiya a wannan yanki na Najeriya a wata shida na dokar.
Sakamakon rikon sakainar kashi da halin ko oho da gwamnatinsa ke yi ga harkar tsaron kasa inda duk da irin halin da tsaro ke ciki amma har yau Shugaba Jonathan, ya kasa nada Ministan Tsaro.
Domin na tabbata in dai irin wannan hali ne na ko oho za a ci gaba da yi a harkar tsaro koda shekara dubu za a yi ana dokar ta-baci to babu abin da zai sauya a wannan yanki, domin ita gwamnati yaudarar jama’a kawai take yi.
Domin haka ’yan Majalisar Dattawa da ’yan Majalisar Tarayya in har kasar ce da ’yan kasar a gabanku, to ya kamata ku kawar mana da wanda muke ganin shi ne matsalar kasar wato Shugaba Goodluck Jonathan.
Shugaba Jonathan yana daga cikin manyan matsalolin Najeriya, domin dokar ta-baci kawai babu abin da za ta haifar inba ana daukar matakan da suka dace ba, musamman tattaunawa da masudauke da makami.
Dokar ta-baci aikin banza ne tunda watanni shida da suka gabata babu abin da ya sauya, baya ga kara munanan hare-haren da masu dauke da makamin suka rika yi. Dole ne sai an dauki matakin da dokar kasa ta fada cewa duk gwamnatin da ta kasa tsare rayuwar ’yan kasa a tsigeta, don haka ku tsige Shugaba Jonathan domin ya gaza, ba zai iya rike Najeriya ba.
Domin ba ya ga rashin tsaro irin satar rashin kunya da mukarraban gwamnatinsa ke yi da satar danyen man fetur da mutanen yankinsa ke yi sun isa a ce majalisa ta tsige shi daga gadon mulki. Yau sata ta zamo ado a kasar nan, misali ana cikin bincikar badakalar daukar kudin talakawa a sayi motoci masu sulke da Ministan Sufurin Jiragen Sama Misis Stella Oduah ta yi a kan Naira miliyan 255, sai Shugaban kasar ya fita waje tare da ita. Kuma bayanai suna fitowa cewa yana kokarin yayyafa wa wutar da ta taso ruwa. Yanzu kuma ga wata ta taso inda Majalisar Dattawa ke zargin bacewar kudin da aka ware domin saukaka wa jama’a radadin karin kudin man fetur da ake kira da Ingilishi (SURE- P) har Naira biliyan 500. Kwamitin Majalisar Dattawa a kan shirin SURE- P da Sanata Abdul Ahmed Ningi, ke jagoranta ne ya gano cewa wadannan makudan kudin talakawa malala gashin tunkiya sun yi batan dabo sama ko kasa a
tsakanin Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) da ofishin Ministan Man Fetur.
Haba jama’a wai shin ina muka fito kuma ina za mu ji ne, shin shugabannin kasarmu barayi ne suka rene ko barayyi ne suka yaye su?
Sata ta rashin kunya da mugunta, na tabbata irin satar da shugabanninmu na Najeriya ke yi ya zarce satar sayen riga ko wando ko aure ko sayen mota, sata ce kawai ta mugunta, mutum ya saci abin da shi da zuriyarsa ba za su iya ci ba. Amma abin takaicin shine gwamnatin Shugaba Jonathan ta kasa hukunta
kowa sai karya da yaudarar talakawa da daure wa barayi gindi take yi. Don haka wakilanmu a majalisa wannan kalubale ne a kanku, in kuma kuka ki sauke nauyin da ke kanku tarihi ba zai yafe muku ba.
Amadu Manager,
Unguwan Karofin Madaki, Bauchi.
08065189242.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno