Lokaci ya yi da za a soke kudin ayyukan mazaba

Kudin aiwatar da ayyukan mazabu da ake biyan ’yan majalisa a Najeriya tun dawowar damokuradiyya ya dade yana tayar da kura. Abin ya yi kamari ne a makon jiya bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bankado cewa an salwantar da fiye da Naira tiriliyan daya wajen aiwatar da wadannan ayyuka […]

Lokaci ya yi da za a soke kudin ayyukan mazaba
Lokaci ya yi da za a soke kudin ayyukan mazaba

Kudin aiwatar da ayyukan mazabu da ake biyan ’yan majalisa a Najeriya tun dawowar damokuradiyya ya dade yana tayar da kura. Abin ya yi kamari ne a makon jiya bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bankado cewa an salwantar da fiye da Naira tiriliyan daya wajen aiwatar da wadannan ayyuka a cikin shekara goma da suka gabata ba tare da ganin wani abu a kasa ba a fadin mazabun da ake da su a nan kasar nan.

Hukumar ICPC ta yi wannan bankadar ce a yayin wani taron bita kan yadda za a kawar da cin hanci a tsakanin ma’aikatun gwamnati da kuma bada kyaututtuka ga wadanda suka nuna hazaka da gaskiya a bakin ayyukansu, wanda ya gudana a Fadar  Shugaban Kasa a Abuja. Kamar yadda aka yi tsammani taron ya samu halartar ’yan Majalisar Dattawa da na Wakilai, wadanda Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe suka jagoranta kuma dukkansu sun tofa albarkacin bakinsu game da wannan zargi, inda suka ce wannan zargi na ICPC ba a kawo shi hade da gamsassun hujjoji ba. Domin a ta bakin su biyun kudin da kuma sa ido kan aiwatar da ayyukan duk suna karkashin Majalisar Zartaswa ce.

An fara aiwatar da wannan shiri na bada kudin ayyukan mazabu ne tun mulkin Shugaba Obasanjo na farko. A wancan lokacin ba a bayar da wani muhimmin dalilin da ya sanya aka kirkiro shirin ba. Amma ko a wancan lokaci jama’a da dama sun yi zargin cewa an samar da shirin ne don toshe bakin wadansu ’yan majalisa da suke kokarin tsige Obasanjo daga kan kujerarsa saboda wasu dalilai nasu.

Saboda haka wannan sabon ikirari da Hukumar ICPC ta yi yana nuni da cewa akwai bukatar a zauna a sake kallon wannan shiri da idon basira. Ja-ni-in-ja-kan da yake faruwa a tsakanin Majalisar Zartaswa da Majalisun Dokoki a tsawon wannan lokaci ta sanya zai iya zama hanyar da ke sanya wannan irin makudan kudade suke salwanta da sunan ayyukan mazabu ba tare da an iya bada bahasi a kansu ba. A mafi yawan mazabu a fadin kasar nan babu wata alama da za ta nuna an aiwatar da wani aikin a mazaba. Kai ko a inda ma aka ce an yi su za ka tarar da aikin amaja ne na babarodo ’yan kwangila suka yi duk da yake an fitar da makudan kudi a kansa.

Maimakon wannan shiri na ayyukan mazabu ya kasance wata hanya ta inganta rayuwar jama’a, yanzu shirin ya kasance wata hanya ta damfara da ’yan majalisa suke amfana da ita. A zahirin gaskiya ma, wannan shiri na bada kudi don yin ayyukan mazabu ya zama wata kafa ta kashe-mu-raba a tsakanin ’yan majalisa da ma’aikatan wasu ma’aikatun gwamnati.

Rahotannin da suka gabata a jaridu da kuma kungiyoyin sa- kai da kuma subul-da-baka da wadansu ’yan majalisa suka yi ya sanya alamar tambaya game da sahihancin wannan shiri. A yayin da suke aikin kasafin kudi a kan kimsa kudade ga kowane dan majalisa a kan aiwatar da wannan aiki sannan daga bisani bayan an amince da kasafin sai a bayar a kwangilar aikin ga wani dan kwangilar da dan majalisar ya kawo, daga karshe kuma kudin sai su fada a lalitar dan majalisar.

Kiran da Shugaba Buhari ya yi kan a samar da wata kotu ta musamman wacce za ta sa ido kan irin wannan badakala a nan bai ma taso ba. Domin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da kuma wasu da ake da su irinsu sun isa su yi maganin wadannan ayyuka a karkashin dokokin da ake da su a yanzu a kasar nan. Lokaci ya yi da kasar nan za ta tantance ko ya dace a  ci gaba da kyale ’yan majalisa da wadansu ma’aikatan gwamnati suna watanda da dukiyar al’umma ko a’a. Duk da yake ’yan majalisa na ikirarin cewa ya dace a ce suna da wani aiki da za su yi kuma su nuna a mazabunsu domin a sake zabensu a zabubbuka na gaba, amma bai kamata aiwatar da ayyukan ta zamo ta hanyar wannan shiri na ayyukan mazabu ba. Kuma ba tare da bata lokaci ba,  ya kamata a gaggauta soke wannan shiri na ba wa ’yan majalisua kudin ayyukan mazabu.

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos