Lokaci ya yi da za a sulhunta da Boko Haram – Zoro

dan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Shugaban Kwamitin Kula da ‘’Yan Gudun Hijira na Majalisar Wakilai Malam Sani Zoro ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi sulhu da kungiyar Boko Haram domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.Malam Sani Zoro ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron masu […]

Lokaci ya yi da za a sulhunta da Boko Haram – Zoro
Lokaci ya yi da za a sulhunta da Boko Haram – Zoro

dan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Shugaban Kwamitin Kula da ‘’Yan Gudun Hijira na Majalisar Wakilai Malam Sani Zoro ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi sulhu da kungiyar Boko Haram domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Malam Sani Zoro ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron masu ruwa da tsaki da Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa (NHRC) ta shirya a Abuja domin duba halin da ’yan gudun hijira suke ciki a kasar nan.
dan majalisar ya ce zai yi wuya a kauce wa aukuwar rikici a duniya, sai dai wajibi ne mutane su rika sulhuntawa, domin “dukkan rikice-rikice suna kawo karshe ne a kan teburin shawarwari.”
Malam Sani Zoro ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta karkatar da dukiyar kasa wajen bunkasa kasa maimakon sayo bindigogi da harsasan da za a yi amfani da su wajen yaki, inda ya ce, “Gasiya akwai bukatar mu yi sulhu da wadannan kangararrun yara.”
Malam Sani Zoro ya ce bayan mutuwar tsohon shugaban kungiyar marigayi Mohammed Yusuf, abin da mayakan suka nema a sake gina musu masallacinsu tare da biyansu diyyar mambobinsu biyar da aka kashe, “wanda abin da gwamnati za ta kashe ba zai fi Naira miliyan hudu ba, amma a yau ga shi mun rasa dimbin rayuka kuma muna ta kashe kudi domin magance hare-haren ta’addancin,” inji shi.