Lokaci ya yi da za mu tuna da kauyukanmu
A wannan makon, matashi kuma hazikin mai sharhi kan al’amuran yau da kulum, Malam Nasir Abbas Babi (08033186727) ya yi mana tambihi ne game da mutanenmu na karkara. Ko me yake cewa? Mu saurare shi:Mutum da mutum ’yan uwan juna ne tun azal, ba wai sai an haife su gida ɗaya ba. Kuma ko wane […]
A wannan makon, matashi kuma hazikin mai sharhi kan al’amuran yau da kulum, Malam Nasir Abbas Babi (08033186727) ya yi mana tambihi ne game da mutanenmu na karkara. Ko me yake cewa? Mu saurare shi:
Mutum da mutum ’yan uwan juna ne tun azal, ba wai sai an haife su gida ɗaya ba. Kuma ko wane ɗan uwa dole za ka same shi yana son ɗan uwansa, a kodayaushe yana kula da shi idan shi ne ke kan gaba. Shi kuma wanda ake kan gabansa yana nuna biyayyarsa ga wanda yake gaba da shi. Idan kuma aka samu akasin haka daga gefe ɗaya, to lalle wanda aka samu giɓi daga gefensa yana da matsala ta jahilci duniyance da addinance ko ƙarancin wayewa.
Ba lalle ba ne wanda ya fi girman shekaru shi ne zai taimaka wa ƙarami ba, ko wanda ke da tarin dukiya zai taimaka wa talaka ba, sai dai wanda duk yake da abin taimakawar da wani ɗan uwansa ke buƙatuwa da shi, to shi ne haƙƙi ya rataya kansa ya taimaka. Kuma yin taimako shi ne kawai zai sa mutum ya kasance mai sauke wajibin da yake kansa a cikin al’umma. Idan ya kasa aikata haka, to ya zama tamkar juji (shara) a cikin mutane. A taƙaice dai, a iya cewa yaro zai iya amfanar da babba, kamar yadda talaka zai iya amfanar da mai kuɗi.
Jahili yana buƙatar taimakon mai ilmi, talakawa da shugabanni na buƙatar taimakon junansu da na masu arziki a cikinsu. Kamar dai yadda aka san duka ɗan Adam ba zai rasa inda yake da naƙasu ba, yake kuma buƙatuwa da taimakon wani a inda ya kasa ɗin.
Duk dai yadda ta kasance, idan mutum yana jin ƙishirwar da ba ya da ikon gusar da ita sai tare da taimakonka, wajibi ne ka ba shi ruwa ya sha, idan girman kai ya hana masa ya karɓa daga gare ka, to yanzu kuma kyautatawa ce idan ka lallaɓe shi, ka fahimtar da shi, kana lurar da shi a kan hatsarin da ke cikin rashin shan ruwan nan. Daga nan idan ya ƙi karɓa har ya halaka, shi ke nan, ya halakar da kansa ke nan. Kai ka yi abin da ake buƙatar ka yi, ka kyautata a fuskar addini da kuma ta zamani.
To sai dai kuma in za ka bayar da taimako, idan gida na so, ai bai dace ka kai daji ba. Mutumin da yake mancewa da mafarinsa kuma ba abin yabo ba ne. Misali, idan mutum ya bar gidansa da ƙazanta, sai ya je yana share hanya yana tsaftace ta don mutane su ji daɗin wucewa, ina ganin sunansa mahaukaci ba mai taimako ba. Kamar dai yadda ɗimbin mutanen ƙauye da ke zaune a birni suka mance da ƙauyukansu.
Yadda tsantsar jahilci na addini da zamani ya yi wa wasu
ƙauyuka yawa, abin haushi ne inda har ta kai za ka ga saurayi ɗan shekara 25 zuwa 30 bai iya karanta Fatiha ba, ko ma tsoho ɗan shekara 70 zuwa sama. Abin mamaki kuma sai ka ji an ce Dokta ko Farfesa wane daga ƙauyen nan ya fito ko kuma Malam wane ko Honourable ko Alhaji wane ai ɗan kauye kaza ne.
Lokaci da yawa idan na tuna da Sani Sabulu a inda yake cewa: “Ni Sani sabulun Haja. Ni na Amina ƙanen Inno. A cikin sana’ar waƙa, ban san ƙauye da ƙauna ba. Tafiya ƙasa ba ta hana min in je ƙauye da gangata. Ba ni mance mutanen ƙauye, don na san jama’ar birni. Ba ni rena mutanen ƙauye, wai don na san jama’ar birni. kauye an ka yi yaye na. kauye an ka yi min aure, sannan Nissan jama’ar birni…” sai in yaba mai sosai kuma in jinjina wa
tunaninsa, a daidai yadda nake ganin kasawar waɗanda suka zo birni suka manta da ƙauye.
Sau da yawa kuma sai in rasa gane waye mai laifi a cikin want ton lamari? Ko shakka babu na tabbatar jama’ar da ke zaune a ƙauyuka suna buƙatar taimakon jama’ar da ke birni ta ɓangarori da dama. kauye ba su da ruwan sha na ƙwarai, ba su da wutar lantarki, ba su da motocin hawa na jin daɗi. kauye ba su da ilmin addini wadatacce balle na zamani.
Abin da ban gane ba shi ne, shin ’yan ƙauye ne da suka dawo birni suka zama wata tsiya, kamar gwamnoni, kwamishinoni, ministoci da wasu ’yan majalisunmu ya fi cancanta su riƙa kai wa ƙauyuka ɗauki; ko kuma ire-irenmu waɗanda tun kaka da kakanni hulɗarmu da ƙauye ta yanke?
A tawa fahimtar, ƙauyuka ne suka haifi birane. Don haka duk ’yan birni asalinsu ƙauye ne. Ashe kuwa ya zama dole mutum ya kula da asalinsa, in dai da hankali da sanin ya kamata. Bai kamata mu bar mutanen ƙauye a matsayin wasu bayin da ke noma mana hatsi da shinkafa muna ci ba, wannan ba adalci ba ne. Koda ko ba ’yan uwanmu na zumunta ba ne a can, to lallai ’yan uwanmu ne a addini.
In ba a nan ba, to tabbas ’yan uwanmu ne na kasancewar mu duka ’yan Adam. Kuma dukkanmu muna da gudunmawar da za mu iya ba su.
A ƙauyuka ne fa za ka samu mata ma’aurata ba su da aikin da ya wuce zuwa rafi ɗebo ruwa. Idan sun dawo gida, daga sussukar hatsi sai daka su ne kawai aikin. Babu ilmin addini balle na boko, don haka sallar ma koda ana yi, ana yin ta ne don tana da wani matsayi a cikin jerin ayyukan yini amma ba don an san muhimmancin ta ba.
Mafi yawan budare mata a ƙauye, idan bayan zuwa gona da rafi, da idan dare ya yi a je wurin gaɗa a dandali, ba su san komai ba. Ba su ma san idan an yi aure ana rayar da sunnar Annabin Allah ba ne, suna yi wa abin wata fahimta ce ta daban.
Ba waɗannan ne kawai matsalolin ƙauyukanmu ba amma dai mu tsaya a nan. Fatar da nake dai, Allah Ya sa wannan tsokaci ya amfane mu kuma ya sanya mu cikin wadanda za su taimaki al’ummar da ke bukatar taimako, ba mu yi ta bata gashiri wurin dahuwar kaho ba. Amin!
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah.
Hidindimun Gizagawa na want ton makon:
A labarin farin ciki, Bagizage Malam Mu’azu Hardawa Bauchi (08062333065), Allah Ya ba shi karuwar haihuwar ’ya mace a ranar Asabar da ta gabata.
Muna rokon Allah Ya raya kuma Ya dayyaba. Amin! – Gizago.
Shi kuwa Garba Garus Bako Jama’are (08079340929) za a daura aurensa ne a yau Juma’a, da misalin karfe 4:15 na yamma. (Allah Ya sanya albarka, Ya ba da zuri’a nagartatta, amin. – Gizago).
A wannan makon, ga wadanda suka samu rijistar shiga kungiyar Gizago: 1-Hadiza Sadauki Sadauki Gusau, Jihar Zamfara, 08188611084 (GZG651ZMF).
2-Muhammad Auwal Yusuf Adam Mariga, Jihar Neja, 08022446864 (GZG652NEJ).