Lokacin da aka ce Jihar Katsina ce ta biyu a talauci sai da na yi kuka –Rabe Darma

Injiniya Muttada Rabe Darma shi ne tsohon Shugaban Hukumar Bundasa Samar da Man fetur ta dasa (PTDF) daga 2008-2012 kuma dan Jam’iyyar PDP a Katsina. A tattaunawarsa da manema labarai a Kaduna, cikinsu har da wakilinmu ya tabo al’amura da dama da suka shafi siyasa da rayuwar jama’ar jiharsa: Ka na ganin shigowar gwamnatin dimokuradiyya […]

Lokacin da aka ce Jihar Katsina ce ta biyu a talauci sai da na yi kuka –Rabe Darma
Lokacin da aka ce Jihar Katsina ce ta biyu a talauci sai da na yi kuka –Rabe Darma

Injiniya Muttada Rabe Darma shi ne tsohon Shugaban Hukumar Bundasa Samar da Man fetur ta dasa (PTDF) daga 2008-2012 kuma dan Jam’iyyar PDP a Katsina. A tattaunawarsa da manema labarai a Kaduna, cikinsu har da wakilinmu ya tabo al’amura da dama da suka shafi siyasa da rayuwar jama’ar jiharsa:

Ka na ganin shigowar gwamnatin dimokuradiyya ya zo da wani ci-gaba a Jihar Katsina?
dwarai kuwa an yi ayyukan ci-gaba da dama, da farko lokacin da gwamnatin dimokuradiyya ta zo, bashin da ake bin Jihar Katsina na da yawa. Bashin da ya fi cin rai shi ne bashin dananan ’yan kwangila. To irin wannan bashin a cikin shekara daya da hawan gwamnatin aka biya da ma wasu manyan basussuka, gwamnatin Katsina ta zauna ba ta da sauran bashi a kanta. Wannan shi ne ci-gaba na farko. Na biyu, lokacin Umaru Musa ’Yar’aduwa, akwai wani taron dara wa juna sani da muka yi a shekarar 2001, inda muka duba tarihin ilimi a Jihar Katsina, tun daga lokacin Shehu Usman dan Fodiyo da abubuwan da suka faru a dasar Katsina, muka gano cewa ai a lokacin da danfodiyo, rabin malaman addini a dasar Hausa ’yan Katsina ne. To ka ga, dila shi ne dalilin da ya sa aka kafa Kwalejin Katsina, saboda Bature ya ga mutanen nan suna da ilimin da za su ride makarantar nan in an kafa ta.  Amma a hankali abin sai ya tabarbare, sai ilimin ya samu koma-baya dwarai da gaske. Ni binciken da na yi a wancan lokacin sai ya nuna min cewa idan mutum 100 za su zauna jarrabawar SSCE mutum uku kawai ke iya cinye jarrabawar. Sai gwamnatin Jihar Katsina ta yi dodarin farfado da ilimin a wancan lokacin, sai aka kafa wani kwamiti wanda kowace makaranta aka kafa mata rukunin da zai rida kula da ita. Kuma kowace makaranta ’yan garin da take ake dauka su kula da ita. To wannan abin ya sa ilimin ya farfado, ya fara komawa kan hanya. Sannan duk wata babbar kasuwa a Jihar Katsina an yi dodarin gina hanyar da ta ratsa kusa da ita don saudada wa jama’a wajen sufuri, da sauran ayyukan ci-gaba da dama. Da gwamnatin Ibrahim Shehu Shema ta zo kuma sai ta dora a kan wadancan ayyukan ta ci-gaba.
Da ka yi maganar ci-gaba, sai muka tuno da wani rahoto da aka fitar cewa Jihar Katsina ce ta biyu wajen talauci, me za ka ce?
To, zai iya yiwuwa, dila abin da suka duba na auna talauci a Jihar Katsina suna da yawa. Amma ni malamin jami’a ne, ba ni iya yi maka magana a kan abin da ba ni da tabbaci a kansa. Jihar Katsina ba abin da ba ta yi min ba, karatun da na yi duk kyauta na yi shi. Jihar Katsina ce ta maida ni mutum cikin hukuncin Allah. Yau duk inda na je na yi magana a dasar nan za a saurare ni. To koda na karanta rahoton cewa Jihar Katsina ce ta biyu a talauci, kuka na yi. Amma kamar yadda na gaya maka ba ni iya tabbatar da wannan rahoto, amma idan yau za ka je gida ka zauna da mutane, in ka ji abin da za su ce, wani rikicin da ke kansa in ka ji sai ka ride baki. Wani ma sai kawai ka ji an ce ya yanke jiki ya fadi, wanda a da hakan ba ta faruwa. To idan ka kalli wancan bangaren, ta yadda mutane ba su iya daukar dawainiyar asibiti ko makaranta da sauransu, to, me za ka ce?  Ni na san a lokacin ina PTDF, asibitin canjin akwai lokacin da wani ya gaya min cewa mutane na fama da matsalar rashin kudin da za a yi musu aiki. Wannan ya sa daga ranar da suka yi min magana, duk wata na rida ba su Naira dubu 500, a rida taimaka wa wanda ba ya da shi. Haka ma a asibitin Turai ’Yar’aduwa, sai mutum ya kawo matarsa haihuwa, amma matsalar Naira 1,500 ta hana a yi mata aiki. A nan ma na rida ba da Naira 250,000 a taimaka wa mutane. Haka ma a babban asibitin Katsina a sashin manyan hadurra, sai a kawo mutum rai hannun Allah, amma sai matsalar Naira 2,000 ta hana likita ya duba shi. Nan ma na rida ba da Naira 300,000 kowane wata a taimaki bayin Allah.
Bayan na gama aikin gwamnati, to akwai wani adashe da ake yi in kana so, za a rida tara maka wani abu a lokacin da kake aiki, idan ka bari sai a ba ka. Da na tashi fita daga PTDF, kudin da na samu sun kai Naira miliyan 121. Na ce to wadannan kudi komawa zan yi gida in saka su ga gina dananan yaranmu da Allah Ya ba hazadar karatu wadanda ke firamare na gwamnati. Saboda ’ya’yan talakawa ne ke karatu a L.E.A. Yara 7,500 suka zauna jarrabawar da muka tsara, daga kowace daramar hukuma. Kuma mun ce ne a dauki duk yaran da ke daukar na daya zuwa na biyar. Yara 100 da suka ci jarrabawar, muka dauki nauyin kai su makarantun kudi muna biya musu. Da na karbi kudin sallama ta kuma, sai na yi tunanin wace hanya ce mutanenmu za su iya amfana da wadannan kudi? Sai muka sayo motoci, mun kashe Naira miliyan 30 a sayen motocin. Muka sa misali inda za ka kashe Naira 500, sai muka ce ka biya Naira 200. Sauran Naira 300 ka sa ta a aljihu ka yi wa iyalin ka tsaraba. Babu abin da ke raina irin taimakon mutanen Jihar Katsina, domin taimako mutanen Katsina taimakon kaina ne. To amma saboda mu ’yan siyasa ba abin da muka iya sai bin juna da sharri, kuma sharrin sai ya dare a kan talaka, sai aka maida maganar sayen motocin siyasa. Na farko, su mutanen da muka yi yarjejeniya da su muka sa hannu, su ne suka ba da direbobin da za su tuda motocin. Wasu ’yan siyasa suka koma bayan fage suka zuga su, suka ce kaza-kaza, an kashe muku kasuwa. Kuma ina so in tabbatar maka, NURTW ta Katsina, ni ban taba zama da su ba, amma su manajojin motocin nan sun zauna da su ya kai sau 15. An yi yarjejeniya aka sa hannu, za ku daukar mana direbobinmu, muka ce mun yarda, amma duk direbobin da za ku ba da sai mun kai wa Road Safety sun tantance su, har da duba su a asibiti. Kowane dire ba sai da muka kashe Naira dubu 40 da wani abu aka ba shi satifiket. Sannan muka je ma’aikatar sufuri da b.I.O, suka ba mu takardar cewa motocinmu sun cancanci su hau hanya. Daga nan muka je hukumar kula da sufuri, suka tura mu wajen hukumar tara kudin shiga, suka ce sai mun biya harajin shekara uku zuwa biyar duk muka biya. Sannan muka dawo ma’aikatar ayyuka suka ba mu satifiket na ku je ku taimaka wa mutane, saboda ba neman kudi za mu yi ba. Kawai sai muka ji a rediyo shugaban NURTW yana cewa wai ba su san da waccan yarjejeniya ba.
Za a iya tunanin cewa gwamnati na yin haka ne saboda tunanin ire-irenka za su iya raba ta da mutane?
A’a, ba mu yundurin dwace jama’a gaskiya. Jama’a na Allah ne, kuma Allah Shi ke yi komai, Shi ke sawa Shi ke hanawa. Ni dai na san komai na Allah ne. Kuma ai akwai mutanen da za ka ga sai sun sha alwashin za su yi kaza, amma su kasa, dole sai Allah Ya so za su iya yi. Ni abin da na ce ma, kamata ya yi gwamnatin Katsina ta rida jawo mutanen da ke son taimaka wa jiharsu a jiki. In ma saboda ya kwashe mutane ne, to sai me, ba dai mutane ake son a taimaka ba?
Idan jama’a Jihar Katsina su ka kawo maka goron gayyata ka tsaya takarar gwamnan jihar, za ka amince?
Da ka bari lokacin ya yi. Saboda ni mutum ne wanda, na yarda da Allah Shi ke yin komai. Misali, ayyuka da dama ban nema ba, ina zaune aka zo aka neme ni. To yanzu ka fara cewa kana neman mudami, ke nan ka raina dodarin da Allah ke maka.
A yadda sabuwar Jam’iyyar APC ke neman mamaye dasar nan, za ka iya shiga ka yi takara a dardashinta idan mutane su ka budaci hakan?
Wato, ina so ku gane cewa ni dan siyasa ne ba dan takara ba. Akwai dan siyasa akwai dan takara. dan takara shi wanda zai samu matsala nan ya koma can. Ni ina PDP, ita na fara ina cikinta duk matsala, mutu-ka-raba takalmin kaza.
Shin me ake nufi da PTDF, kuma mene ne tasiri ko amfaninta ga al’umma?
Wato PTDF wani asusu ne wanda aka ajiye domin ya taimaka wajen fasahar ilimin hado man fetur. Lokacin da aka gano man fetur a Najeriya, har kusan shekara 50 wadanda ke wannan aikin Turawa ne, wadanda su suke da ilimin hadowa da sarrafawa. To ita PTDF tun daga 1973 aka kafa ta. Amfaninta kawai shi ne ta taimaka wa ’yan Najeriya su samu wannan ilimi na hadowa da sarrafawa. Har na shekara uku a wajen ban taba zuwa NNPC ba. Wani ma dubana ya yi ya ce ai tunda mun yi ritaya ya san yanzu mun mallaki rijiyar mai. Na yi dariya kawai na ce masa wallahi ban ma san yadda ake ba da ta ba.

Shin wane ne Injiniya Muttada Rabe Darma?
Kamar yadda kuka sani, sunana Alhaji Muttada Rabe Darma. Kuma an haife ni a cikin garin Katsina a Unguwar Darma. Na yi firamare a Rafindadi Primary School, wadda a yanzu ta koma Waziri Zayyanu Model Primary Shcool. Daga nan na wuce sakandaren dofar ’Yandaka daga nan na shiga Jami’ar Bayero ta Kano.Da na gama injiniyar kanikanci a Jami’ar Bayero, Allah Ya taimake ni, sashin suka dauke ni koyarwa.  Na koyar na tsawon shekaru shida zuwa bakwai, kuma ina koyarwar na na je na yi digiri na biyu a Jami’ar Benin ta Jihar Edo a yanzu. Da na gama sai na sake dawowa Jami’ar Bayero na yi digiri na biyu kan hulda da jama’a da cinikayya. A 1996 na bar aiki da Jami’ar Bayero na koma Hukumar Wutar Lantarki ta dasa (NEPA) na shekara daya. Da na bar NEPA sai na koma kamfanin Al-Am Oil Company a Fatakwal, na yi aikin wata uku.Na bari na koma kamfanin sayar da motoci na Coscharis a matsayin Manaja Sashin Hada-Hadar Kudi na Kamfanin. Daga nan Asusun Rarar Man Fetur (PTF) ya dauke ni aikin tuntuba (Consultant), a lokacin ne na yi aiki tsakanin Katsina da Yola.
Bayan an rushe PTF, a shekara ta 2000 gwamnatin Jihar Katsina, a dardashin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ta ba ni aiki a ofishin Gwamna a matsayin daraktan bincike, wato duk abubuwan da gwamnati za ta yi, sai a turo mana mu duba, mu zagaya cikin mutane, a darshe mu gano wadannan abubuwan za su yi tasiri ga mutane? To na yi wannan aikin daga shekarar 2000 zuwa 2002. Daga nan aka ba ni Darakta na Hukumar SEPA, na yi shekara daya da ’yan watanni. A watan Agusta shekarar 2003 aka nada ni Kwamishinan Raya Karkara da Harkokin Matasa. A shekara ta 2006 da Kwamishinan Ayyuka ya sauka zai yi takara, sai aka dara min ma’aikata biyu ke nan, na yi wata bakwai ina kula da ma’aikatiu biyu a matsayin Kwamishina.
Bayan yi zaben shekarar 2007 a watan Fabrairu 2008, sai Uwargidan Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa wato Hajiya Turai ’Yar’aduwa ta ba ni aikin kula da mata da matasa a ofishinta. Sai kuma na samu shugaban Asusun PTDF daga 17 ga Nuwamba 2008 zuwa 17 ga Nuwamba 2012, kuma na yi wannan aiki na shekara hudu, kuma Allah Ya sa an gama lafiya.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna