Lokacin da mata suka fara kunar bakin wake

An fara samun rahoton mace ta shigar harkar kunar bakin wake a jihar Gombe a ranar Lahadi 8 ga watan Yunin wannan shekarar, inda wata mata dauke da bam ta kashe kanta da wani soja a kusa da barikin soja na bataliya ta 301 da ke Gombe. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito […]

Lokacin da mata suka fara kunar bakin wake
Lokacin da mata suka fara kunar bakin wake

An fara samun rahoton mace ta shigar harkar kunar bakin wake a jihar Gombe a ranar Lahadi 8 ga watan Yunin wannan shekarar, inda wata mata dauke da bam ta kashe kanta da wani soja a kusa da barikin soja na bataliya ta 301 da ke Gombe. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, matar ta boye bam din ne a cikin hijabinta ta rungume soja bam din ya tashi da su gaba daya.
A kasar Falasdinu aka fara samun mata sun shiga harkar kunar bakin wake, inda aka samu wata mai suna Wafa Idris ‘yar kungiyar Fatah, wadda ta tayar da bam a tsakiyar  Jerusalam a shekarar 2002, inda ta hallaka mutum guda tare da jikkata fiye da mutum 100. Sai kuma Zainab Abu Salem, ‘yar shekara 18 da ta tayar da bam a watan Satumbar shekarar 2004, a lokacin da wani dan sandan Isra’ila ya dunfare ta yana son ya duba Jakarta, inda bam din ya hallaka ta da dan sandan, ya kuma raunata mutum 30.
Tun lokacin da ‘yan kunar bakin wake suka kai wa tgwayen benayen nan na Amurka hari a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 malamai da dama suka bayar da fatawar cewa kunar bakin wake ya saba wa musulunci kuma duk wanda ya aikata haka wuta za shi.