Lokacin da shugabanni za su kwashe kudin kanannan hukumomi ya wuce – Gwamna Lalong
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa lokacin da shugabannin kananan hukumomin jihar za su kwashe kudaden kananan hukumominsu su azurta kansu ya wuce. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake rantsar da sababbin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar 17 a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.Gwamna Lalong ya ce […]
Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa lokacin da shugabannin kananan hukumomin jihar za su kwashe kudaden kananan hukumominsu su azurta kansu ya wuce. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake rantsar da sababbin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar 17 a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.
Gwamna Lalong ya ce “Mun rushe tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Jihar Filato ne, don mu dakatar da irin almundahanar da suke yi da kudin al’umma. Wannan sabuwar gwamnati ba za ta tsaya tana kallo shugabanni suna almundahana da kudin kananan hukumomin ba. Musamman idan aka dubi irin mawuyacin halin da al’ummar jihar nan suke ciki da kuma irin kudirorin da wannan gwamnati ta sanya a gaba na ganin ta dawo da zaman lafiya da kyautata rayuwar al’ummar jihar.”
Gwamna Lalong ya ce an nada sababbin shugabannin rikon ne bisa lura da cancantarsu. Don haka ya yi bukaci su rike wannan amana da aka damka musu tsakani da Allah a shugabancin da za su gudanar a yankunansu.
Ya ce “Ina gargadinku kan ku sani cewa yanzu ba lokaci ba ne da za a shiga ofis a azurta kai da dukiyar al’umma ba, wannan lokaci ya wuce. Don haka ina shawartarku ku tsaya wajen ganin kun fuskanci irin matsalolin da suke damun al’umma a yankunanku. Ku kammala ayyukan raya kasa da aka fara kuma ku biya albashin ma’aikata.”