‘Lokacin kawo ƙarshen haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya ya yi’

An bukaci horas da jami’an tsaro dabarun yaki da hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya.

‘Lokacin kawo ƙarshen haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya ya yi’

Gwamnatin Oyo ta yi kira da cewa lokaci ya yi na kawo ƙarshen haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya a jihar.

Gwamnatin ta yi wannan kiran ne a yau Laraba yayin wani taron yini ɗaya da aka gudanar tare da masu ruwa da tsaki a kan matsalar haƙar ma’adanai ta haramtacciyar a Jihar Oyo.

 

Cikin jawabinsa ga mahalarta taron, Darakta-Janar na hukumar bunkasa haƙar ma’adanai a  Jihar Oyo, (OYSMIDA), Injiniya Abiodun Oni ya ce tuntuni aka gano cewa haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanya yana kawo zagon ƙasa ga tattalin arzikin jihar da Gwamnatin Tarayya.

A yayin taron wanda aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, Injiniya Oni ya ce haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya tana shafar lafiyar al’ummomin da ke zaune a wuraren da ake haƙo ma’adanan, musamman ibtila’in zaizayar ƙasa.

Ya ce haƙar ma’adinai ba da izni ba ya jefa miliyoyin jama’ar jihar cikin damuwa alhali gwamnati ba ta amfana da komai cikin irin wannan haramtaccen aiki.

Dangane da hakan ne Injiniya Oni ya ce nauyin kawo ƙarshen wannan matsala ya rataya a wuyan gwamnatin jihar da dukkan masu riƙe da masarautun gargajiya.

Ya ce akwai buƙatar kowanne daga cikin waɗannan shugabanni su sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar bayar da gudunmawarsu a kan fafutukar yaƙi da haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya a Jihar Oyo.

A nasa jawabin, Kwamandan Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Oyo, Mista Padonu Augustine ya ce yanzu haka Kwamanda-Janar, Dakta Ahmed Abubakar ya kammala aikin tuntubar ma’aikatar ma’adanai ta kasa a kan horas da jami’an rundunar dabarun yaƙi da haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanya.

Ya ce a shirye suke wajen gudanar da aikin daƙile irin wannan aiki da zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin jihar da ma kasa baki daya.

Aminiya ta ruwaito cewa, sarakunan yankin da ake haƙar ma’adinai a jihar su ne sahun gaba-gaba a taron, inda suka bayar da shawarwarin da suke ganin idan an yi aiki da su za a cimma nasara.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe