Lokacin kawo karshen barace-barace ya yi

A kwanakin baya, Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Suleiman Adamu ya yi tsokaci a kan kokarin da ake yi na kawo karshen matsalar nan mai wuyar sha’ani ta almajirai. Ya ce sarakunan gargajiya na yin duk wata mai yiwuwa don ganin sun kawo matsalar nan ta bara a kan tituna ta hanyar kawar da almajiranci a […]

Lokacin kawo karshen barace-barace ya yi
Lokacin kawo karshen barace-barace ya yi

A kwanakin baya, Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Suleiman Adamu ya yi tsokaci a kan kokarin da ake yi na kawo karshen matsalar nan mai wuyar sha’ani ta almajirai. Ya ce sarakunan gargajiya na yin duk wata mai yiwuwa don ganin sun kawo matsalar nan ta bara a kan tituna ta hanyar kawar da almajiranci a jihar. Sarkin ya furta hakan yayin da yake karbar bakuancin wakilan kungiyar daliban manyan makarantu karkashin shirin nan na tsarin almajiranci, wanda ke da hankoron ilmantar da jama’a game da illolin da kuma matsalolin da ke tattare da barace-barace a kan tituna da almajirai ke haddasawa. Ya jinjina wa Shirin Tsarin Almajiran kan abin da ya kira tunkarar matsalar gaba-gadi, tare da kiran wasu kungiyoyin taimakon al’umma da shiga sahun fafutikar kawo karshen bara a kan tituna.

Shirin Tsarin Almajirai na Kasa, reshen Jihar Bauchi sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar 25 ga watan Mayu don tunawa da Ranar ‘Yancin Almajirai. Sun rike alluna dauke da rubutun cewa: ‘Kowane da yana da damar samun ingantaccen ilmi’. ‘Almajiri shi ma zai iya samun kowane matsayi cikin al’umma’. Sakataren Shirin Tsarin Almajiran, Abubakar Salisu ya bayyana bukatar iyaye su dauki daukacin nauyin ‘ya’yansu kuma bai kamata su bari ‘ya’yan nasu su zama bata gari a cikin alumma ba.

Haka ita ma Majalisar Dattijai a ranar Talata 28 ga watan Mayu, ta yi kiran da a yi sauyi game da tsarin ilmin almajirai da ake amfani da shi a halin yanzu a yankin Arewa. Shugaban Zauren na da, Sanata Ahmad Lawan, wanda ya gabatar da kudurin, ya ce dokar samar da ilmi ga kowa ta shekarar 2004, wacce ta yi tanadin dole ne kowane yaron da shekarunsa suka kai ya yi karatun boko, to wajibi ne a aiwatar da ita yadda ya dace. Ya ce: “Da akwai yaran da suka kai shekara 17, da suke gararamba a kan tituna, maimakon zuwa makaranta, suna daukar darasi.” Ahmad Lawan ya ce lokaci ya yi da jihohin da al’amarin almajiranci ya yi kamari, su bullo da sabbin matakai da tsare-tsaren da za su kawo karshen kazancewar al’amarin na almajiranci.

Da yake magana game da batun almajircin a lokacin taron Ranar ‘Yancin Almajirai na bana da aka gudanar a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, Daraktan Kungiyar Kare Hakkin Almajirai (ACRI) Malam Nurudeen Lemu, ya ce matsalar almajiran idan ba a yi hankali ba za ta kasance gagarumar annoba ga Najeriya, har sai Gwamnatin ta tashi haikan wajen yakar matsalar. Malam Lemu ya ce: “Akwai bukatar mu gane cewa almajirci matsala ce da tasirin rashin kyawun shugabanci ya haifar kuma almajiran sun zama wadanda lalacewar kyakkyawan  tsarin gudanar kasa ya fi shafa. Don haka, lallai ne mu gano bakin zaren matsalar, tun yanzu.”

A Arewa, a can baya, tsarin almajirancin ya tafi yadda ake so, sai dai a ‘yan shekarun nan, kusan tsarin ya gama rasa alkibla. A halin yanzu, tsarin na da kalubale iri-iri da suka hadar da na tsarin abin da za a koyar, da daliban kansu da kuma na malaman ma; wanda dukkan wadannan suke matukar bukatar gagaruman sauye-sauye. Mafi girman lokacin da yaran ke bukata domin koyon Al’kur’anin, yana karewa ne a barace-baracen kan tituna. Bugu da kari, tsarin na cike ne da rashin kwararrarun malamai, da ke kare fahimtarsu game barace-baracen. An dai yi ta samun korafe-korafe da dama a kan almajiran da suka rasa ko dai idonsu ko hannuwansu, a sakamakon mugun hukuncin da malamansu ke dauka game da laifukan da suka aikata. Almajirai da dama sun rasa rayukansu ta dalilan cuta ko kuma yunwa, yayin da wasu kuma ke salwanta ta dalilan aikata miyagun laifuka a kansu ko kuma ta hanyar samun su a kan tituna.

Lalacewar tsarin almajirancin ya ci gaba da bunkasa, sakamakon yadda iyaye marasa tunani, wadanda daukar almajirancin a zaman hanyar kauce wa sauke hakkokin nauyin da ya rataya kansu na iyaye, su ke samun malaman da ke a shirye su karbi yaran a matsayin almajirai. Katse wannan mugun tsarin na bukatar gwamnati ta fito da hukunci mai tsauri tare da samar da dokokin da suka dace da yadda za a yi aikin. Kasancewar matsala ce yanki, dole ne kowace jihar yankin Arewa ta kirkiro da ba wai kawai dokokin da za su gudanar da al’amarin ba, a’a lallai ne su kafa dokokin da za su haramta bara a kan tituna da almajiran ke yi, da nufin taka birki ga almajiran da ke hijira zuwa jihohin da babu dokokin haramta bara.

Kasancewar al’amarin wata barazana ga kasa nan gaba, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi zagi wajen magance matsalar. Nauyi yana sargafe a kan wuyan Shugaba Muhammadu Buhari da ya kira taron kolin masu ruwa da tsaki a batun don dakile matsalar. Ya kamata dukkanin masu ruwa da tsaki da ke da jibi da batun kamar Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci (NSCIA) da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) da Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi (ALGON) da kuma Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohin Arewa, lallai ne su hada karfi da karfe wajen lalubo matakan da suka kamata su dauka. Shugaba Buhari yana da babbar damar kawo karshen almajiranci a kasar nan. Dole ne ya yi amfani da wannan damar tasa don ya bar kyakkyawan tarihi.